Da duminsa: Ana artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a jihar Imo

Da duminsa: Ana artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a jihar Imo

- Da alamun abubuwa na cigaba da munana a yankin kudu maso gabas

- Kusan kulli yaumin sai an kai hari ofishin yan sanda a kasar Igbo

- Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu a harin yau

Tsagerun yan bindiga da ake zargin matasan IPOS/ESN ne sun shiga artabu da jami'an runduna ta musamman watau 'Special Forces' bayan bankawa ofishin yan sandan Orji, dake Owerri, wuta.

Misalin karfe 12 na rana, yan bindiga sun dira unguwar Orji dake birnin jihar kuma suka bankawa ofishin yan sanda wuta.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa Vanguard cewa kawo misalin karfe 12:55 na ranar Talata, sun ga yan bindiga sanye da kaya mai launin baki da ja suna kona ofishin yan sandan.

Wannan abu ya rutsa da iyayen yara da suka je daukan yaransu daga Makaranta.

A riwayar Punch, harsashi ya bugi wata mata sakamakon wannan artabu da yan bindigan keyi da jami'an tsaro.

Matar ta kasance mai sayar da kaya a kusa da inda ake artabun.

Yanzu haka gawarta na kwance a kasa yayinda makwabta ke rusa kuka.

DUBA NAN: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Da duminsa: Ana artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a jihar Imo
Da duminsa: Ana artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a jihar Imo
Asali: Original

KU KARANTA: Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar da 'yayansa 10 rana guda

Wannan hari ya biyo bayan harin da wasu tsagerun ya bindiga suka kai Iwolo Oghe, ofishin hukumar yan sanda Najeriya dake Ezeagu, jihar Enugu.

Guardian ta tattaro cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyar a mumunan harin da suka kai daren Litinin, 24 ga Mayu, 2021.

Bayan haka yan bindigan sun bankawa ofishin yan sandan wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel