Da duminsa: Kuma dai! Tsageru sun hallaka mutum 5, sun kona ofishin yan sanda kurmus

Da duminsa: Kuma dai! Tsageru sun hallaka mutum 5, sun kona ofishin yan sanda kurmus

- Kusan kullum yanzu sai an kai hari ofishin yan sanda a kudu maso gabashin Najeriya

- Wannan karo an yi rashin akalla rayuka biyar

- Har yanzu hukumar yan sanda bata kama mutum ko daya cikin masu harin ba

Wasu tsagerun ya bindiga sun kai hari Iwolo Oghe, ofishin hukumar yan sanda Najeriya dake Ezeagu, jihar Enugu.

Guardian ta tattaro cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyar a mumunan harin da suka kai daren Litinin, 24 ga Mayu, 2021.

Bayan haka yan bindigan sun bankawa ofishin yan sandan wuta.

KU KARANTA: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Da duminsa: Kuma dai! Tsageru sun hallaka mutum 5, sun kona ofishin yan sanda kurmus
Da duminsa: Kuma dai! Tsageru sun hallaka mutum 5, sun kona ofishin yan sanda kurmus
Asali: Original

DUBA NAN: Babban Limanin jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda

A riwayar TheNation akwai yan sanda cikin wadanda aka kashe a harin.

Jaridar ta ce yan bindigan sun kona motoci da dukiyoyin dake cikin ofishin yan sandan.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da harin.

Ya ce bai da cikakken bayani har sai kwamishanan yan sandan jihar, Mohammed Aliyu, ya samu.

A bangare guda, haɗakar jam'iyyun siyasa CUPP, ta kira yi shugaban ƙasa Buhari da yayi murabus daga kujerarsa saboda ya gaza wajen daƙile matsalar tsaron dake ƙara taɓarɓarewa a Najeriya.

A wani jawabi da shugaban kwamitin yaɗa labarai na CUPP, Chukwudi Ezeobika, ya fitar, yace ya kamata Buhari yayi murabus saboda gazawar gwamnatinsa ta APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel