Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda

Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda

- Wani katin gayyatar aure a jihar Borno ya sanya mutane magana a kafafen ra'ayi da sada zumunta

- Wani shahrarren Malami a garin Maiduguri na shirin aurar da 'yayansa 10

- Jama'a sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan daurin aure

Wani shararren Malamin addini, wanda shine Limamin jami'ar Maiduguri, Dr. Imam Goni Muhammad Ali Gabchiya, ya saki katin gayyata zuwa daurin auren yaransa 10 a rana guda.

Wannan kati da Legit.ng ta gani, wani matashi mai suna Comr Mahmud Muhammad ya daura wannan kati a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 23 ga Mayu.

Muhammad ya ce za'ayi wannan daurin auren ne ranar 5 ga Yuni a Masallacin jami'ar Maiduguri inda aka gayyaci daukacin al'umma.

DUBA NAN: Dole mulki ya bar Yankin Arewa bayan wa’adin Buhari – Jigon APC ya na goyon ‘Yan Kudu

Babban Limanin jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda
Babban Limanin jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda Credit: Cmr Mamhu Muhammad
Asali: Facebook

DUBA NAN: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

"Iyalan Sheikh Dr. Imam Goni Muhammad Ali Gabchiya na gayyatarku zuwa daurin auren 'yayansa masu suna kamar haka," ya ce.

Sunan da ya bayyana na maza sune: "Ali Muhammad Ali Gabchiya (Malam Bana), Irbad Muhammad Ali Bin Gabchiya, Muktar Muhammad Ali Gabchiya, Malik Muhammad Ali Gabchiya, da Shafi Ibn Gabchiya Muhammad Ali Gabchiya.

Na mata kuma: Fatima Muhammad Ali Gabchiya, Zubaidah Muhammad Ali Gabchiya, Busaina Muhammad Ali Gabchiya, Haizuran Muhammad Ali Gabchiya, da Haula Muhammad Ali Gabchiya.."

Mun fahimci cewa Sheikh Gabchiya Kanuri ne kuma an haifesa a birnin Makkah, kasar Saudiyya.

Yanzu haka yana zama a Maiduguri kuma shine Limamin jami'ar UNIMAID.

A wani labarin kuwa, wata mata ta yanke shawarar canza labarin aure ta wani siga da ba a san shi ba.

Matar da ba a gano ko wacece ba ta auri maza 7 ita kadai.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na @blog_street, matar da dukkan mazajen nata suka kewayeta ta bayyana cewa tana kula da bukatunsu ita kadai kuma har ta gina wa kowannensu gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng