Wani mutumi ya haukace a banki, yayi zigidir kan kudinsa N300,000 da aka zaftare

Wani mutumi ya haukace a banki, yayi zigidir kan kudinsa N300,000 da aka zaftare

- Wani uba ya haukace cikin banki kan zaftare masa kudi da akayi kuma aka ki gyarawa

- A cikin farfajiyar bankin, mutumin ya tube kayansa saboda fushi da bacin rai

- Mutumin ya lashi takobin cewa ba zai bari a cigaba da aiki a bankin ba sai an mayar masa da kudinsa

Bidiyon wani mutumi dan Najeriya da ya tayar da tarzoma cikin banki kan zaftare masa kudi N300,000 daga asusunsa ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta.

Wani matashi mai suna Gbemi Dennis, ya daura bidiyon a Tuwita inda yace kimanin wata daya kenan mutumin ke kai korafi bankin amma basu magance matsalar ba.

A bidiyon, mutumin ya kai yaransa bankin domin nunawa ma'aikatan cewa ya gaza biyan kudin makarantansu sakamakon abinda ya faru.

DUBA NAN: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Wani mutumi ya haukace a banki, yayi zigidir kan kudinsa N300,000 da aka zaftare
Wani mutumi ya haukace a banki, yayi zigidir kan kudinsa N300,000 da aka zaftare @GbemiDennis
Asali: Twitter

Mutumin ya bayyana cewa ya dade yana kai korafi bankin, amma basu magance matsalar sun mayar masa da kudi ba.

Wani jami'in tsaron bankin ya yi kokarin kwantarwa mutumin hankali amma abin yaci tura.

Bayan haka, mutumin ya fita daga cikin ofishin zuwa farfajiyar bankin inda ya fara tube kayansa yana mai cewa ba zai bari su cigaba da ayyukansu ba.

DUBA NAN: Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda

Kalli bidiyon:

Yayinda wasu yan Najeriya ke fadin cewa ya kamata a magance masa matsalar, wasu na cewa da yiwuwan mutumin ne yayi wasa da katinsa na ATM kuma yan damfarar yanar gizo suka kwashe masa kudi.

A wani labarin kuwa, rundunar yan sandan reshen jihar Imo ta ce ta kama wasu mutum biyu mambobin kungiyar wadanda suka kware wurin yi wa bankuna fshi a jihar da kewaye.

Kwamishinan yan sandan jihar, Abutu Yaro, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ya ce kama yan fashin na cikin umurnin da mukadashin sufeta janar na kasa, Usman Baba ya bada na cewa a dakile miyagun da ke adabar mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel