Wasu Ƙwararrun Ƴan Fashin Banki Sun Shiga Hannun Ƴan Sanda

Wasu Ƙwararrun Ƴan Fashin Banki Sun Shiga Hannun Ƴan Sanda

- Yan sanda a jihar Imo sun kama wasu mutum biyu cikin wata tawagar masu fashin bankuna

- An kama su ne a mabuyarsu da ke garin Eziobodo da ke karamar hukumar Owerri ta jihar Imo a ranar Talata

- Bayan kama su, yan sandan sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 da harsashi da riga da hankici mai launin kayan sojoji

Rundunar yan sandan reshen jihar Imo ta ce ta kama wasu mutum biyu mambobin kungiyar wadanda suka kware wurin yi wa bankuna fshi a jihar da kewaye, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar, Abutu Yaro, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ya ce kama yan fashin na cikin umurnin da mukadashin sufeta janar na kasa, Usman Baba ya bada na cewa a dakile miyagun da ke adabar mutane.

Wasu Kwararru Yan Fashin Banki Sun Shiga Hannun Yan Sanda
Wasu Kwararru Yan Fashin Banki Sun Shiga Hannun Yan Sanda. Hoto: @MobilePunch
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a garin Eziobodo da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma na jihar.

Kwashinan yan sandan ya ce, "An yi kamen ne a ranar Talata 11 ga watan Mayun 2021 bayan da yan sandan Operation Puff Adder II suka samu bayan sirri daga wurin yan sa-kai game da miyagun da suka kware wurin fashi da jihar da kewaye.

"Nan take yan sanda suka garzaya zuwa mabuyarsu, da isarsu sun nemi bude musu wuta amma suka ci galaba a kansu. Sakamakon musayar wutar mutum biyu cikin yan fashin sun mutu yayin da saura suka tsere da raunin bindiga.

KU KARANTA: Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

"Abubuwan da aka gano a wurin sun hada da AK-47 daya, harsashi magazin biyu da jaka dauke da riga da hankici mai launin kayan sojoji.

"Da ake musu tambayoyi, wadanda ake zargin biyu sun amsa cewa suna cikin wata kungiyar yan fashi da suka kware wurin yi wa bankuna fashi. Sun kuma ambaci sunayen abokan aikinsu da a yanzu yan sanda ke farautarsu."

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164