Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano

Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano

- Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa aƙalla mutum 64 ne suka jikkata lokacin da wata tankar mai ta fashe a Sharaɗa

- An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda abun ya shafa sun zo kallon yadda motar ta faɗi ne kafin daga baya ta fashe

- Hukumar kashe wuta a jihar Kano, ta tabbatar da faruwar lamarin, tace jami'anta takwas na cikin waɗanda abun ya shafa

Aƙalla mutum 64 ne sukaji raunuka kala daban-daban bayan wata motar dakon mai ta fashe a jihar Kano.

KARANTA ANAN: Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro

Dailytrsut ta ruwaito cewa tankar man fetur ɗin ta fashe sannan ta kama da wuta yayin da take sauke mai a gidan man Al-Hisan dake titin Ali Gusau, unguwar Sharaɗa cikin garin Kano.

Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano
Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daga cikin waɗanda suka samu raunin akwai jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano waɗanda suka kawo ɗauki cikin gaggawa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

KARANTA ANAN: AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Rahoto ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka samu raunukan mazaunan unguwar ne.

An gano cewa waɗanda suka samu raunin sun zo kallon yadda motar ta faɗi kuma take ci da wuta kafin daga bisa ni ta fashe.

Duk da cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa, amma aƙalla mutum 64 ne suka jikkata kuma yanzun haka suna amsar kulawa a asibitin Murtala dake Kano.

Kakakin hukumar kashe wuta ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace jami'an hukumar su 8 na cikin mutum 64 da abun ya shafa.

A wani labarin kuma Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya tsige sarkin Pauwan Katsina hakimin ƙanƙara daga muƙaminsa.

Sarkin ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gano cewa hakimin na da hannu a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262