Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro

Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro

- Tsohon shugaban rundunar soji, Tukur Buratai, yayi alhinin rasuwar Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama

- Buratai yace magajin nasa ya ɗakko hanyar da zai sanya Najeriya alfahari a ɓangaren tsaron da take fama da shi

- A ranar Jumu'a, shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru ya rasa rayuwarsa a wani hatsarin jirgin sama da ya ritsa dashi a Kaduna

Tsohon shugaban rundunar soji, Tukur Buratai, yace magajin sa, Ibrahim Attahiru, ya kama hanyar sanya Najeriya alfahari.

KARANTA ANAN: Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Mr. Buratai yace marigayin ya ɗakko hanyar kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a ƙasar nan kafin wannan mummunan lamarin yayi sanadiyyar mutuwarsa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro
Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya bayyana hatsarin da abin tausayi ga yan Najeriya, yace Mr. Attahiru da jami'an da suka rasu tare da shi sun bar tarihin da ba za'a taɓa mantawa dashi ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cewarsa, hatsarin yayi matuƙar girgiza shi kamar yadda ya girgiza yan Najeriya saboda Mr. Attahiru ya mutu amma yabar mutane da yaƙinin irin nasarorin da ya samu a ɓangaren ayyukan soji.

KARANTA ANAN: Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Buratai yace:

"Attahiru ya kama hanyar sanya ƙasar mu alfahari bisa najimin ƙoƙarin da yake yi wajen magance matsalar tsaron da muke fama da ita, bani da tantama a kan ƙwazon shi saboda yayi aiki a ƙarƙashina a ɓangare daban-daban."

"Nayi matuƙar kaɗuwa da baƙin cikin mutuwar Janar Ibrahim Attahiru, a hatsarin jirgin sama, wanda ya riƙe muƙamai da dama kafin zaman shi shugaban rundunar soji."

"A madadin iyalaina ina miƙa saƙon ta'aziyya ga shugaban ƙasa Buhari, iyalan shi, ministan tsaro, jami'an sojin ƙasa da na sama bisa mutuwar waɗannan manyan jami'ai yayin da suke cikin aiki."

Buratai ya roƙi hukumomin tsaro su tabbatar da ayyukan da waɗannan mutanen suka ɗakko bai tafi a banza ba, ta hanyar cika musu burinsu a ayyukan da suka fara.

A wani labarin kuma COVID19: Mutum 60,000 Kacal Saudiyya Ta Amince Zasu Yi Hajjin Bana a Duniya

Ƙasar saudiyya ta bayyana adadin mahajjatan da zasu samu damar yin aikin hajji a wannan shekarar ta 1442 byan hijira, wacce tazo dai-dai da 2021.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da hukumar hajji ta ƙasa ta futar a shafiɓta na dandalin sada zumunta facebook 'National Hajj Commission Of Nigeria.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel