Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga

- Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya tsige sarkin Pauwan Katsina hakimin ƙanƙara daga muƙaminsa

- Sarkin ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gano cewa hakimin na da hannu a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa jihar

- A kwanakin baya dai majalisar sarkin ta dakatar da hakimin Kanƙara, Alhaji Yusuf Lawal, daga muƙaminsa bisa zarginsa da taimakawa yan bindiga

Majalisar sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ta tumɓuke rawanin hakimin ƙanƙara biyo bayan gano cewa yana da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

Katsina Daily post ta wallafa a shafinta na facebook cewa masarautar ta gano sarkin Pauwan Katsina kuma hakimin ƙanƙara, Alhaji Yusuf Lawal yana taimaka wa wasu yan bindiga wajen gudanar da ayyukan ta'addacin su.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga
Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga Hoto: Katsina Dailypost Fb fage
Asali: Facebook

Bisa wannan dalilin ne majalisar sarki ta tsige shi daga muƙaminsa na Sarkin Pauwa hakimin kankara kwata-kwata.

KARANTA ANAN: Da duminsa: An gano abinda ya kawo hatsarin jirgin marigayi Janar Attahiru a Kaduna

Legit.ng hausa ta gano cewa a kwanakin baya majalisar sarkin ta dakatad da hakimin bisa zarginsa da hannu wajen taimaka wa yan bindigan dake kai hare-hare a faɗin jihar ta Katsina.

A rahoton da katsina daily post ta ruwaito ya nuna cewa sakataren fadar mai martaba sarkin Katsina kuma sarkin yaƙin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, shine ya tabbatar da tsige hakimin.

A wani labarin kuma IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar kawo hari Abuja da Plateau.

Kakakin hukumar yan sanda, Mr Frank Mba, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ranar Juma'a a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel