Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike
- Hukumar AIB ta bayyana cewa ta samu nasarar gano akwatin dake naɗar bayanai da murya yayin da jirgi ke tafiya a sama
- Hukumar tace zata sauke duk abinda ke ciki sannn tayi nazari akansu domin gano musabbabin hatsarin jirgin
- Rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa rashin kyawun yana yi ne ya jawo hatsarin jirgin wanda yayi sanadiyyar mutuwar COAS, Attahiru
Hukumar binciken haɗurra ta ƙasa AIB-N, ta bayyana cewa ta gano wani baƙin akwati na jirgin da yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojin Najeriya, Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10.
KARANTA ANAN: Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru
Hukumar tace ta gano FDR da CVR waɗanda ke naɗar bayanai da murya yayin da jirgi ke tafiya a sararin sama, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
A wani jawabi da manajan yaɗa labaran AIB, Tunji Oketumbi, ya fitar ranar Asabar, yace suna cigaba da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin.
An yiwa jawabin take da "AIB-N zata gudanar da binciken hatsarin jirgi." kamar yadda punch ta ruwaito.
Jawabin yace: "Mun gano FDR da CVR na jirgin saman NAF da yayi hatsari, amma a halin yanzun muna cigaba da bincike."
"Masu binciken zasu sauke muhimman bayanan dake cikin FDR da CVR ɗin, sannan su yi nazari akan su a ɗakin bincike na AIB dake babban birnin tarayya, Abuja."
KARANTA ANAN: Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah
Rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa jirgin ya faɗi ne sabida rashin kyaun yana yi.
A ranar Asabar ɗin data gabata ne aka yi jana'izar shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru tare da sauran jami'ai 10 da suka rasa ransu sanadiyyar hatsarin jirgin sama.
A wani labarin kuma Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga
Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya tsige sarkin Pauwan Katsina hakimin ƙanƙara daga muƙaminsa.
Sarkin ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gano cewa hakimin na da hannu a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa jihar.
Asali: Legit.ng