'Yan Boko Haram Na Shirin Kai Hare-Hare a Abuja Da Jos, IGP

'Yan Boko Haram Na Shirin Kai Hare-Hare a Abuja Da Jos, IGP

- Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria ya sanar da kwamishinonin Abuja da Plateau cewa yan ta'adda na shirin kai hari a yankunansu

- Sufetan na yan sanda ya ce bayannan sirri da ya samu ya nuna wani Muhammad Sani da Suleiman ne za su jagoranci kai harin

- Don haka, sufeta janar din ya umurci kwamishinonin biyu su tsaurara matakan tsaro musamman a kusa da gine-ginen gwamnati

Mukadashin Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria, Usman Baba, ya ankarar da kwamishinonin babban birnin tarayya Abuja da jihar Plateau kan yiwuwar hari daga yan kungiyar Boko Haram, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan ya sanar da su ne cikin wata sako da ya aike wa kwamishinonin biyu mai dauke da sa hannun babban jami'insa, Idowu Owohunwa mai mukamin mukadashin CP.

'Yan Boko Haram Na Shirin Kai Hare-Hare a Abuja Da Jos, IGP
'Yan Boko Haram Na Shirin Kai Hare-Hare a Abuja Da Jos, IGP. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Dole Manoma Su Fara Aiki a Gonakinmu Kafin Nasu, Dogo Giɗe da Black

Ya ce bayannan sirri sun nuna cewa yan ta'addan suna shirin kai hari a Abuja da Jos.

Sakon mai lamba TB: 0900/IGP.SEC/ABJ/VOL.TI/47 an mata lakabi ne da 'Yan ta'adda za su fadada harinsu.'

Wakilin majiyar Legit.ng ya samu kofi na sakon a ranar Juma'a.

A cikin sakon, mukadashin na IGP ya umurci kwamishinonin yan sandan su yi bitar tsarin tsaronsu su kuma tsaurara matakan tsaro musamman a gine-ginen gwamnati a Abuja da Jos.

KU KARANTA: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Sakon ya ce, "Bayanan sirri da sufeta janar na yan sanda ya samu ya nuna yan ta'addan Boko Haram na shirin kai hari a manyan birane a kasar, musamman a Jos, Plateau da FCT, Abuja.

"Wadanda za su jagoranci kai hari sune Muhammad Sani, kwamandan Boko Haram da ke zaune a dajin Sambisa da mataimakinsa, Suleiman, wanda ke buya a Lawan Musa Zango, Gashua, jihar Yobe.

"Don haka, Sufetan Janar na yan sanda na umurtar ku da kuyi bitan tsarin tsaronku musamman kusa da gine-ginen gwamnati da ke yankunanku domin kare afkuwar mummuna shirin yan ta'addan.

"Ku kasance lafiya."

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel