Zamfara: Dole Manoma Su Fara Aiki a Gonakinmu Kafin Nasu, Dogo Giɗe da Black
- Shugabannin yan bindiga a jihar Zamfara sun bawa manoma umurnin su fara aiki a gonakinsu kafin daga bisani su noma nasu
- Wani mazaunin Zamfara ya ce mutanen wasu yankuna a garin sun tafi gonakin Dogo Gide da Black domin fara sharar gona
- Ya ce shugabannin yan bindigan sun basu tabbacin cewa za su kyalle su suyi noma tare da basu kariya muddin sun fara aikin a gonakinsu
Manyan shugabannin yan bindigan jihar Zamfara, Dogo Gide da Black 'Baki' sun ja kunnen manoman wasu yankuna akan cewa sai sun fara musu aikin gonakinsu kafin su bar su suyi nasu a wannan daminan.
Domin gujewa abinda zai kai ya kawo, Daily Trust ta gano cewa wasu daga cikin mazauna yankunan sun fara aiki a gonakin shugabannin yan bindigan tun yanzu.
DUBA WANNAN: Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano
Wani mazaunin garin Dansadau mai suna Bilyaminu Dansadau ya sanar da Daily Trust cewa wasu daga cikin manoman kauyukan dake kusa da Babbar Doka dake kusa da Dansadau a karamar hukumar Maru, sun fara zuwa gonar Dogo Gide domin gyaranta.
"Sun fara tattara kansu domin su tafi gonar Dogo Gide a ranar Asabar. Shugaban yan bindigan, tunda farko ya shaidawa manoman su fara aiki a gonarsa kafin ya kyalle su su noma gonakinsu.
"Manoman sun kosa su fara aiki duba da cewa damina ta karato. Yan bindigan sun tilastawa manoman barin gonakinsu. Yan bindigan sun kashe manoma da dama sun sace wasu sun raunata wasu.
"Dogo Gide da dakarunsa suna zama ne a dazukan Kaduna, Kebbi da Zamfara. Kwanakin baya wasu mazauna kauyukan sun gan shi ya hallarci sallar Juma'a a garin Babbar Doka," in ji shi.
Kazalika, wani mazaunin garin mai suna Babangida Magami ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa manoma cike da manyan motocci uku daga Kurar mota, Ruwan Mesa, Unguwar Makeri, Mai Taushi Danbaure, Hayin Madi da Chabi a makon da ta gabata sunyi aiki a gonar wani hatsabibin shugaban yan bindiga mai suna 'Black'.
KU KARANTA: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa
Shima Black ya shaida musu cewa babu wanda zai yi noma har sai an fara noma masa gonarsa. Ya kuma yi alkawarin zai basu kariya idan suka bi umurninsa.
"Manoman sun gyara gonakin shugabannin yan bindigan a ranar Litinin da ta gabata yanzu suna jiran ruwa ya sauka domin su yi musu shuka," in ji Magami.
Kakakin rundunar yan sandan Zamfara, SP Muhammadu Shehu ya ce zai yi bincike kan batun. "Ku bamu lokaci mu bincika," in ji shi.
Kwamishinan Labarai, Alhaji Ibrahim Dosara ya ce gwamnati bata da masaniya kan batun.
"Ba mu da masaniya kan batun," in ji shi.
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.
Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.
Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.
Asali: Legit.ng