Kudaden da aka wawure: FG ta samo sama da $700m a cikin shekaru 4, Malami
- Ministan sharia' kuma antoni janar Abubakar Malami yace Najeriya ta samo sama da dala miliyan 700 na kudadenta da aka wawure
- Kamar yadda ministan ya sanar, yace sun samo kudin ne cikin shekaru hudu kuma zasu cigaba da kokarin ganin sun karbo sauran
- Malami yace kwashe kudin kasar nan da ake yi ana kaiwa kasashen ketare na daga cikin dalilin fatara, rashin tsaro, tabarbarewar ilimi da sauransu
Abubakar Malami, antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, ya ce gwamnatin tarayya ta samo sama da dala miliyan 700 a cikin shekaru hudu na daga cikin kudaden da aka wawure.
Ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wani taron da aka yi kan shige da ficen kudi ba bisa ka'ida ba da kuma samo su wanda hukumar yaki da rashwa mai zaman kanta (ICPC) ta shirya.
Malami yace kasashen da ke tasowa a Afrika suna rasa sama da $148 biliyan ga rashawa a kowacce shekara, The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kotu, sun yi awon gaba da alkali a Katsina
"Najeriya ta hanyoyin da take bi da kuma hadin kan wasu kasashe, ta samu an dawo da sama da dala miliyan 700 daga Amurka, Ingila, Bailiwick ta Jersey, Switzerland da Ireland a cikin shekaru hudu da suka gabata," yace.
"Har a halin yanzu muna aiki da wasu kasashen ketare domin tabbatar da cewa an dawo da dukkan kadarorin Najeriya dake can."
Malami wanda ya samu wakilcin Juliet Ibekaku-Nwagwu, babban mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin shari'a, ta jajanta yadda manyan kudade ke fita daga Afrika ba bisa ka'ida ba wanda hakan yasa rashin tsaro ke cigaba da tsananta sannan ake rasa cigaba.
"Babu shakka, wannan fitar kudin ke kawo rashin cibiyoyin lafiya da ilimi, talauci da rashin ababen more rayuwa a kasashen Afrika," ya kara da cewa.
KU KARANTA: Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki
A wani labari na daban, duk da ikirarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram kuma ta kwace yankin arewa maso gabas, bayanan da ake samu daga wasu gwamnoni abun tsoro ne.
Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed a 2019 ya ce dakarun sojin kasar nan cike da nasara sun ci galaba kan mayakan Boko Haram.
Ya ce Najeriya na fuskantar sabon salon rashin tsaro ne wanda ya zama ruwan dare dama duniya. Sai dai a halin yanzu akwai jihohin da ke fama da hare-hare wanda ake zargin na 'yan ta'addan Boko Haram ne ke kaiwa, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng