Duk da FG na ikirarin murkushe Boko Haram, ga jihohi 6 da ake zargin sun kutsa kai

Duk da FG na ikirarin murkushe Boko Haram, ga jihohi 6 da ake zargin sun kutsa kai

Duk da ikirarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram kuma ta kwace yankin arewa maso gabas, bayanan da ake samu daga wasu gwamnoni abun tsoro ne.

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed a 2019 ya ce dakarun sojin kasar nan cike da nasara sun ci galaba kan mayakan Boko Haram. Ya ce Najeriya na fuskantar sabon salon rashin tsaro ne wanda ya zama ruwan dare dama duniya.

Sai dai a halin yanzu akwai jihohin da ke fama da hare-hare wanda ake zargin na 'yan ta'addan Boko Haram ne ke kaiwa, Premium Times ta ruwaito.

Ga jerin jihohi shida da ake zargin mayakan ta'addancin Boko Haram ne suka kutsa:

KU KARANTA: Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi

Duk da FG na ikirarin murkushe Boko Haram, ga jihohi 6 da ake zargin sun kutsa kai
Duk da FG na ikirarin murkushe Boko Haram, ga jihohi 6 da ake zargin sun kutsa kai. Hoto daga @Buharisallau1@daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai

Bauchi

Jihar Bauchi tana yankin arewa maso gabas ne kuma ta koka da yadda aka lalata sabis dinta na MTN dake karamar hukumar Gamawa ta jihar inda take zargin Boko Haram da hannu a ciki.

Tuni dai gwamnatin jihar Bauchi ta alakanta wannan harin da miyagun hare-haren da 'yan Boko Haram ke kawai Geidam dake jihar Yobe.

Jigawa

Bayan harin da aka kai jihar Bauchi, gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga mazauna jihar da su bude idanunsu bayan rahoton da aka samu na shiga miyagun 'yan ta'adda cikin jihar.

Bayan wannan rahoton, Gwamnan jihar Jigawa, Badaru yayi taro da sarakunan gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da jami'an tsaro inda yace su kai rahoton duk wani abun zargi da basu fahimta ba a jihar.

Kano

A wata yammacin Lahadi ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da damke wasu mutum 13 da ake zargin mayakan Boko Haram ne a yankin Hotoro na jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa, Mohammed Yerima, wanda ya bada sanarwan yace birged ta uku dake jihar Kano ne suka kama su.

Jihar Kano kuwa tana da iyaka da jihohin Jigawa da na Bauchi wadanda suka bayyana damuwarsu a kan shigar mayakan ta'addanci jiharsu.

Niger

Gwamnan jihar Neja da kanshi ya tabbatar da cewa miyagun mayakan Boko Haram ne suka samu shiga jiharsa. Ya bayyana cewa mayakan ta'addanci sun kafa tuttocinsu a kananan hukumomin Kaure da Shiroro na jihar.

Ya kara da tabbatar da cewa a kalla 'yan ta'addan sun kori mazauna yankuna sun kai 3,000 inda suka yi gudun hijira, jaridar Guardian ta ruwaito.

Nasarawa

Tuni Gwamnan jihar Nasarawa ya koka da yawan hare-haren da yake zargin mayakan ta'addancin Boko Haram ne ke kaiwa a jiharsa.

Wannan lamarin kuwa ya kawo tsananin firgici da dimuwa ga mazauna babban birnin tarayya ganin cewa suna makwabtaka da jihar.

Benue

Har ila yau, a yayin da Gwamnan jihar Nasarawa yake bayyana cewa 'yan Boko Haram na kai hari cike da nasara a jiharsa, ya tabbatar da cewa suna tsakanin iyakar jiharsa da ta Benue.

A wani labari na daban, wani rahoto da jaridar Leadership ta fitar ya bayyana cewa mai baiwa Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti shawara ta musamman a fannin ilimi, Farfesa Francisca Aladejana ta rasu.

Legit.ng ta tattaro cewa, Aladejana wacce ita ce tsohuwar shugaban kwalejin ilimi dake Ikere, jihar Ekiti, ta rasu ne a ranar Litinin, 17 ga wata Mayun 2021.

Kamar koyaushe, mamaciyar ta isa ofishinta da safiyar Litinin amma sai ta yanke jiki ta fadi yayin da take amsa waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng