Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki

Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki

- Kakan Dangote na daya daga cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara amfani da banki

- Alhaji Alhassan Dantata ya bude asusun banki kuma ya zuba makuden kudade a jihar Kano

- An ga tsoffin rasit kuma kamar yadda aka gano, kudin da ya zuba rakuma suka dauka

Kakan mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yana daya daga cikin 'yan Najeriya da suka fara amfani da banki bayan da aka bude shi.

Kamar yadda wani tsohon rasit ya nuna wanda Nigeria Stories ta wallafa a shafinta na Twitter, dan kasuwan ya zuba kudin ne yayin da aka bude Bankin Turawa wanda yanzu shine First Bank karon farko a jihar Kano a shekara 1929.

KU KARANTA: Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki
Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki. Hoto daga @Nigeriastories
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tashin hankali: Hadimar gwamna ta yanke jiki ta fadi a ofishinta, ta mutu a take

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ko a wancan lokacin, Alhaji Alhassan Dantata ya nuna tsabar kudinsa kuma ya tabbata babban attajiri. Ya laftawa rakuma 20 sisin azurfa inda suka kai bankin.

Wannan labari kuwa ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta yayin da masu tsokaci suka dinga tofa albarkacin bakinsu.

@YOUNGYUPPIE22 martaninsa cewa yayi: "Ina kinibabbun da suka dinga sharara mana karya akan dukiyar Dangote? Su fito su bamu bayani dalla-dalla a kan wannan."

@sidiq_elkanawi ya rubuta: "A takaice wannan mutumin Alhaji Alhassan Dantata mahaifin kakan Dangote ne. Dangote dan jikansa ne."

@thesurrogate2 cewa yayi: "A can inda nayi makaranta na gane cewa Aliko Dangote bai fito daga tsatson matalauta ba. Da yawa daga cikin masu maganganu basu san da iyalan Dantata ba. A gaskiya ni na san shi ne a Aliko Dantata, bayan dawowata Najeriya naji an ce da Aliko Dangote yake amfani."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya tace ta bankado jaridu 476 na yanar gizo da suka sadaukar da ayyukansu kowacce rana wurin fitar da labaran bogi na yaki da gwamnati.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Mayu a Abuja yayin da ya karba bakuncin jami'an NIPR da suka ziyarcesa.

Legit.ng ta tattaro cewa Mohammed ya ce babban abun bada mamakin da aka bankado shine yadda ake kokarin fitar da bayanin bogi kan lafiyar kwakwalwar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel