Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kotu, sun yi awon gaba da alkali a Katsina
- Miyagun 'yan bindiga sun kutsa zauren kotu a kauyen Bauren Zakat dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina
- Sun yi awon gaba da alkalin kotun mai suna Alhaji Husaini Samaila a ranar Talata wurin karfe 3 na yammaci
- Kamar yadda aka gano, gwamnati ta mayar da kotun zuwa karamar hukumar Safana ne saboda rashin tsaro
'Yan bindiga sun yi garkuwa da alkali a cikin kotun Sharia dake kauyen Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Kamar yadda ganau suka sanar da Daily Trust, maharan sun balle kotun inda suka shiga wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma suka yi awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama'ila.
An mayar da kotun shari'ar ne karamar hukumar Safana saboda dalilan tsaro.
Har yanzu dai ba a san dalilin da ya kai alkalin kotu ba duk da yajin aikin da kungiyar ma'aikatan shari'a na Najeriya (JUSUN) ke ciki.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake kwashe daliban jami'a da ba a san yawansu ba
KU KARANTA: Batancin ga Annabi: Duk da shigar 'yan sanda, ana cigaba da rikici a Legas
Katsina tana daya daga cikin jihohin yankin arewa maso yamma da 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka.
Har a halin yanzu jami'an tsaro basu yi martani kan aukuwar lamarin ba.
Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun shiga yajin-aiki, har an kai ga rufe kotu da-dama a Najeriya.
Shugaban kungiyar malaman shari’a na bangaren jihar Legas, Kehinde Shobowale Rahamon, ya bayyana abin da ya sa ma’aikatan su ka tafi yajin-aiki.
Mista Kehinde Shobowale Rahamon ya ce har yanzu doka ta 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai ba ta fara aiki ba har yanzu.
A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Kogi ta yamma, yace shugaban kasa Muhammadu koyaushe baya nan kuma bashi da lokaci.
Jigon jam'iyyar PDP yace ba zai yuwu shugaban kasan ya ki yi wa kowa magana ba sai ta bakin masu magana da yawunsa, TheCable ta wallafa.
Ya ce shirun Buhari na da matukar illa ga yaki da rashin tsaro a kasar nan. Melaye ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawar da aka yi da shi a AIT ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng