Gwamnan PDP Ya Yi Rajista a Makarantar Ƙera Takalma a Jiharsa

Gwamnan PDP Ya Yi Rajista a Makarantar Ƙera Takalma a Jiharsa

- Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya yi rajista a matsayin dalibi a makarantar kera takalma a Aba

- Ikpeazu ya yi kira ga yan Nigeria su rika alfahari da kayayyakin da ake kerewa a kasashensu ta hanyar amfani da su

- Gwamnan ya kuma yi alkawarin bada gudunmawa na fili da wasu abubuwan domin ganin an fadada makarantar

Sha'awar da Gwamna Okezie Ikpeazu ke yi wa kayayyakin da ake kerawa a gida Nigeria ta saka shi ya yi rajista a matsayin dalibi a ranar Laraba a makarantar koyar da kera takalma ta Aba Footwear Academy, Vanguard ta ruwaito.

Da ya ke amsa tambayoyi bayan rajistan, Gwamna Ikpeazu ya bukaci yan Nigeria su rika alfahari da nasu suna siyan kayan da ake yi a Nigeria a matsayin wani mataki na habbaka tattalin arziki.

Gwamnan PDP Ya Yi Rajista a Makarantar Ƙera Takalma a Aba
Gwamnan PDP Ya Yi Rajista a Makarantar Ƙera Takalma a Aba. Hoto: @Vangaurdngr
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger

Ya ce idan har yan Nigeria ba su goyon bayan nasu suna alfahari da kayan da ake kerawa a kasar kawai za su rika taimakawa tattali arzikin wasu kasashen ne.

Ya kara da cewa sai yan Nigeria sun fara siyan kayayyakin sannan yan wasu kasashen za su fara sayan su.

A cewarsa, Aba za ta iya gogaya da China da wasu manyan kasashe a bangaren kera takalma yana mai cewa nan gaba babu wanda zai juya wa takalman Aba baya.

Ya ce ya yi farin cikin ganin makarantar kuma ya yi alkawarin bada gudunmawa domin ganin ta cigaba.

Ya ce zai bada fili wanda za a fadada makarantar domin ta samu daman daukan wasu sabbin dalibai da za a horas.

KU KARANTA: Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

Gwamnan ya yaba da basirar wadanda suka kafa makarantar ya kuma nanata cewa akwai bukatar hadin gwiwa tsakaninsu da makarantar takalma ta Enyimba Automated Shoe Factory.

A jawabinsa tunda farko, wanda ya kafa makarantar, Mr Bentley Chukwuemeka ya bada gwamnan tabbacin cewa za su mayar da hankali domin kera takalma masu nagarta da horas da dalibai da za su cigaba da tabbatarwa Aba ta bunkasa wurin kera takalma.

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel