Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

- Mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da wasu fasinjoji sun tsallake rijiya a baya a bayan jirginsu ya samu matsala bayan tashi

- Jirgin da ya tashi daga filin jiragen sama na Kano, MAKIA, ya tashi zai tafi Abuja ne a ranar Talata amma matsala ta sa ya yi saukar gaggawa mintuna 10 bayan tashi

- Wasu fasinjojin da ke cikin jirgin sun ce sun firgita sosai bisa afkuwar lamarin har ta kai ga sun fasa tafiyar sun koma gidajensu

Fasinjoji da dama ciki har da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin Max Air da ya tashi daga Kano zai tafi Abuja ya samu matsalar inji mintuna 10 bayan tashi daga filin jirgin Kano, MAKIA.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jirgin na Max Air mai lamba VM1645 wanda ya kamata ya tashi karfe 1.30 na rana amma aka yi jinkiri mintuna 30.

Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari
Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dattawan Arewa Sun Goyi Bayan Gwamnonin Kudu, Sun Ce Dole a Dena Kiwo a Fili

Daga baya jirgin ya tashi misalin karfe 2 na rana da fasinjoji cike maƙil.

An gano cewa jirgin ya fara jigiga a iska kimanin mintuna 10 bayan tashinsa hakan yasa ya yi saukar gaggawa.

Wasu majiyoyi sun ce matsalar inji ne ya janyo lamarin wasu kuma suka ce tsuntsu ne ya yi karo da jirgin.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Dr Sama'ila Suleiman, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke jirgin ya ce da ƙyar suka sha yana mai danganta lamarin da sakaci a ɓangaren kamfanin jiragen.

Mr Suleiman ya ce ya ji wani irin sauti na daban a lokacin da jirgin ke tashi amma ya dai bai ce komai ba.

KU KARANTA: Yakin Aiki: Gwamna El-Rufai Ya Gaza Kama Wabba a Kaduna

Ya kara da cewa irin wannan firgicin da suka fuskanta ya saka fasinjoji da yawa cikinsu fasa tafiyar suka koma gidajensu.

Kamfanin Max-Air bata ce komai ba game da lamarin har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164