Gwamnatin Buhari tayi batan basira, Gwamnan jihar Bauchi

Gwamnatin Buhari tayi batan basira, Gwamnan jihar Bauchi

- Gwamna Bala AbdulKadir na Bauchi ya caccaki gwamnatin Buhari ranar Sallah

- Bala ya ce ko yaki da rashawan da Buhari ke ikirarin yi duk buge ne

- Ya ce zargin da gwamnonin kudu suka yiwa Buhari gaskiya ne

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi batan basira kan yadda zata magance matsalar tattalin arzikin kasar.

Bala ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar bayan Sallar Idi da ya halarta ranar Alhamis, domin murnar karewar azumin Ramadana, rahoton Punch.

A cewarsa: "Ina tunanin gwamnatin tarayya ta yi batan basira kan yadda zata ingantatattalin arziki. Abinda suka iya kawai shine tuhumar wasu. Ko yaki da rashawan da suke ikirarin yi ba yi suke ba."

Gwamna Bala ya daura laifin koma bayan da ga kasar nan ke fama da shi kan gwamnatin Buhari, inda yace babu adalci wajen nadin mukamai.

KU DUBA: An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai

Gwamnatin Buhari tayi batan basira, Gwamnan jihar Bauchi
Gwamnatin Buhari tayi batan basira, Gwamnan jihar Bauchi Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Ya kara da cewa: "Akwai wasu miyagun ba a isa a taba su a gwamnatin Buhari ba.. Idan babu adalci a gwamnatinka, idan akwai kabilanci inda bangare daya kadai ake ba mukamai, lallai za'a samu matsala."

"Akwai kamshin gaskiya cikin abinda gwamnonin kudu suka fadi cewa ana fifita wasu sassan kasar nan kan wasu."

"Abinda muka sani a gwamnatin tarayya shine ayi daidaito. Idan babu adalci a sama, ba za'a samu a kasa ba. Sai mun nuna adalci da daidaito zamu iya inganta tattalin arziki."

A bangare guda, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya amsa bukatar gwamnonin kudu na cewa ya shirya taron gangami na kasa da kuma kafa hukumar yan sanda na jihohi.

Kwanaki biyu da suka gabata, gwamnonin kudancin Najeria 17 sun hadu a Asaba, jihar Delta, inda suka tattauna matsalar tsaro kuma suka mika bukatarsu ga gwamnatin tarayya.

Gwamnonin sun bukaci haramta kiwon fili a kudu, kuma sun yi kira ga shugaban kasan ta shirya taron gangami na musamman, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel