Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

- Shugaba Buhari ya yi Sallar Eidul Fitr a birnin tarayya Abuja

- Manyan jami'an gwamnati sun halarci Sallan da akayi a fadar shugaban kasa

- Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa na kokari wajen magance matsalar tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatinsa na namijin kokarin wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

A bayaninsa, Buhari yace yana fatan yan Najeriya zasu gane irin kokarin da sukeyi.

Buhari ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai bayan halartan Sallar Idi a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja, rahoton Channels TV.

Buhari yace za'a magance matsalar yan bindiga da masu garkuwa da mutane kafin a fara samun matsalar rashin abinci.

"Da kudi da jaruman da muke da shi, muna namijin kokari. Muna fatan yan Najeriya za su fahimci wannan matsalar," Buhari yace.

"Yan Najeriya sun sani cewa dubi ga yadda abubuwa suke lokacin da muka zo a 2015, za'a san cewa mun yi kokari wajen tsaro da tattalin arziki."

Ya yi kira ga yan Najeriya su kara hakuri kan yadda lamura suke a yanzu a kasar.

DUBA NAN: Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal

Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari
Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi

A bangare guda, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya amsa bukatar gwamnonin kudu na cewa ya shirya taron gangami na kasa da kuma kafa hukumar yan sanda na jihohi.

Kwanaki biyu da suka gabata, gwamnonin kudancin Najeria 17 sun hadu a Asaba, jihar Delta, inda suka tattauna matsalar tsaro kuma suka mika bukatarsu ga gwamnatin tarayya.

Gwamnonin sun bukaci haramta kiwon fili a kudu, kuma sun yi kira ga shugaban kasan ta shirya taron gangami na musamman, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel