An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai

An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai

- An damke wasu kasurgumin mai safarar bindiga dan kasar Nijar

- Ya bayyana cewa ya sayarwa yan Najeriya kimanin bindigogi 5000

- An bayyana yan bindiga gaban manema labarai a jihar Zamfara

Jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar damke tsagerun yan bindiga biyar wadaanda suke garkuwa da mutane, satar shanu da kuma barandanci.

Ana zargin wadannan yan bindiga na cikin wadanda suka addabi jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Kogi da Neja.

Daga cikin makaman da aka kwace hannunsu akwai bindigogin AK47 guda hudu, ma'aijin albursai 9, albursai 960, da kuma guru da layu, rahoton TVC.

Daga cikinsu akwai direban motan da yake kai musu mutane mabuyarsu kuma a biyashi N200,000 kan kowani mutum da ya kai.

Hakazalika akwai wani dan kasar Nijar, Shehu Ali Kachalla, wanda kasurgumin mai sayar da makamai ne kuma ya fi shekara uku yana safarar makamai.

A cewarsa, ya sayar da akalla bindigogi 4500 ga yan bindiga a Arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila

An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai
Hoto: @tvcnewsng
An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai
Asali: Twitter

DUBA NAN: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Sannan akwai Abubakar Ali na jihar Neja wanda ke aikata nashi ta'asan da karamar hukumar Kagarjo da Chikun na jihar Kaduna.

Ya ce shekaransa uku kenan yana wannan aiki kuma ya kashe mutane biyar da aka ki biyan kudin fansansu.

A cewarsa, shugabansu na biyansu N600,000 zuwa N700,00 kan kowani garkuwa da mutanen da aka samu kimanin milyan 26.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatinsa na namijin kokarin wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

A bayaninsa, Buhari yace yana fatan yan Najeriya zasu gane irin kokarin da sukeyi.

Buhari ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai bayan halartan Sallar Idi a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja, rahoton Channels TV.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng