Wajibi ne Buhari ya saurari abinda muke fada masa, Gwamnonin Kudu 17
- Gwamnonin kudancin Najeriya 17 sun aikewa shugaba Buhari sakon kar ta kwana
- A Najeriya, akwai jihohi 23 a Arewa da 17 kudancin kasar
- Gamayyar gwamnonin kudun sun gana a jihar Delta kan matsalar tsaro
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya amsa bukatar gwamnonin kudu na cewa ya shirya taron gangami na kasa da kuma kafa hukumar yan sanda na jihohi.
Kwanaki biyu da suka gabata, gwamnonin kudancin Najeria 17 sun hadu a Asaba, jihar Delta, inda suka tattauna matsalar tsaro kuma suka mika bukatarsu ga gwamnatin tarayya.
Gwamnonin sun bukaci haramta kiwon fili a kudu, kuma sun yi kira ga shugaban kasan ta shirya taron gangami na musamman, dss.
A hirar da yayi da AriseTV, Akeredolu ya yo fashin baki kan abubuwan da gwamnonin suka bukata daga Buhari kuma yace akwai takwarorinsu na Arewa da sukayi na'am da hakan.
Ya ce da kamar wuya fadar shugaban kasa tayi watsi da abinda suka bukata.
DUBA NAN: Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal
DUBA NAN: Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
"Wajibi ne a saurari duk abinda muka bukata, wajibi ne a amsa. Hakan na nufin fadar shugaban kasa za tayi dubi ciki," yace.
"Na san shugaban kasa. Wajibi ne ya amsa. Saboda ba zaka iya banza da adadin wadannan gwamnoni ba. "
A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatinsa na namijin kokarin wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
A bayaninsa, Buhari yace yana fatan yan Najeriya zasu gane irin kokarin da sukeyi.
Buhari ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai bayan halartan Sallar Idi a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.
Asali: Legit.ng