Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Ya Mutu Yayin Tiƙa Rawa Wurin Ɗaurin Aure

Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Ya Mutu Yayin Tiƙa Rawa Wurin Ɗaurin Aure

- Wani mutum ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tika rawa a wurin daurin aure a Rivers

- Da farko dai mutanen da suke kallonsa suna masa tafi yayin da ya ke rawar sun dauka duk salon rawa ne lokacin da ya fadi

- Sai dai daga bisani bayan an lura ya yi kokarin tashi amma ya sake fadi anyi kokarin kai masa dauki amma wani likita daga baya ya ce ya mutu

Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke tika rawa a wurin bikin aure a Borokiri, kusa da tsohuwar birnin Port Harcout a jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Mutumin mai suna Dein, jagoran mutane ne daga Ataba a karamar hukumar Andoni a jihar.

Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Ya Mutu Yayin Tiƙa Rawa Wurin Ɗaurin Aure
Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Ya Mutu Yayin Tiƙa Rawa Wurin Ɗaurin Aure. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf

Lamarin ya faru a ranar Litinin yayin bikin auren dan uwansa daga Ataba wanda ya auri wata mata daga garin Asarama a karamar hukumar Andoni.

An ruwaito cewa a yayin da mutane ke zaune a wurin daurin auren, mutumin sanye da kaya masu launin fari da baki ya tashi ya fara kayatar da mutane da rawa.

Bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta a ranar Talata da Legit.ng ta gani ya nuna mutumin yana rawa kuma mutane na masa tafi kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi a kasa.

Da farko mutanen da ke zaune ba su motsa ba don suna tunanin fadin da ya yi duk cikin rawar ne inda mai jawabi wurin taron shima ya ke ba'a yana cewa watakila duk rawa ne.

Kamar yadda ya ke a bidiyon, mutumin ya yi yunkurin motsa hannunsa da kansa kamar yana kokarin tashi amma ya sake fadi kasa ya dena motsi.

Bayan yan mintuna kadan mutane sun garzaya inda ya ke a kwance domin su duba abin da ke damunsa.

KU KARANTA: An Yi Rige-Rigen Jefar Da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya

Mai jawabi wurin taron wato MC ya ce, "Likita zai duba shi ya gani ko barasa ne."

An ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka hallarci taron likita ne kuma shine ya tabbatar da mutuwar mutumin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya ce ya ga bidiyon amma a yanzu babu wanda ya shigar wa yan sanda rahoto a hukumance.

A wani labarin daban kun ji wani ofishin rundunar ƴan sandan Nigeria yana can yana ci da wuta a karamar hukumar Bende a jihar Abia.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari ofishin ƴan sandan a safiyar Alhamis.

An gano cewa maharan sun ƙona dukkan motoccin da ke harabar ofishin kafin suka cinnawa ginin wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel