An Yi Rige-Rigen Jefar Da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya

An Yi Rige-Rigen Jefar Da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya

- Mutane da dama a Indiya sun yi watsi da gumakan da suke bauta wa saboda sun gaza kare su daga annobar korona

- Hakan na zuwa ne a yayin da annobar ta wanzu a kasar a baya-bayan nan inda kawo yanzu ta hallaka mutum fiye da miliyan 20

- Asibitoci a kasar na Indiya sun cika makil hakan kuma ya janyo karancin magunguna da gado domin kwantar da marasa lafiya

Mutane da dama a kasar Indiya sun zubar da gumakan da suke bautawa a tituna a yayin da adadin wadanda ke kamuwa da cutar korona ke karuwa a kasar sannan cutar na cigaba da kisa.

Wasu yan kasar sun nuna bacin ransu ga gumakan da suke bautawa tare da yi musu hidima amma sun gaza kare su daga annobar ta korona kamar yadda Shiawaves ta ruwaito.

An Yi Rige-Rigen Jefar da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya
An Yi Rige-Rigen Jefar da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya. Hoto: Shia Waves
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

Sun rika yin addu'o'i ga gumakan da suke bautawa suna masu imanin za su kare su daga kwayar cutar amma daga karshe sun gano cewa abin da suke nema bai samu ba sai suka yi watsi da su.

Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a kowanne rana a Indiya ya kai 3,3780 sannan adadin wadanda cutar ta halaka ya dara miliyan 20.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

Asibitoci a kasar na Indiya sun cika makil hakan kuma ya janyo karancin magunguna, iskar oxyegen da gado domin kwantar da marasa lafiya.

Rashin samun gado a asibitin da karancin magungunan ya janyo wasu masu jinyar suna galabaita sosai ko rasa rayukansu ba tare da sun samu taimakon da suke bukata ba.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: