Yanzu-Yanzu: An Sake Cinnawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta a Abia
- Wasu ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda a ƙaramar hukumar Bende a jihar Abia
- Maharan sun ƙona motoccin da ke harabar ofishin ƴan sandan kafin suka cinnawa ginin wuta
- Ana zargin mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB masu son kafa Biafra ne amma sun musunta hakan
Wani ofishin rundunar ƴan sandan Nigeria yana can yana ci da wuta a karamar hukumar Bende a jihar Abia.
Daily Trust ta ruwaito cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari ofishin ƴan sandan a safiyar Alhamis.
DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kai Samame Maɓuyar IPOB Sun Kama Babban Kwamanda
An gano cewa maharan sun ƙona dukkan motoccin da ke harabar ofishin kafin suka cinnawa ginin wuta.
Ofishin ƴan sandan yana wajen kofar hedkwatar karamar hukumar Abia ne misalin mita 10 daga filin ƙaramar hukumar.
Harin na zuwa ne ƙasa da awanni shida bayan gwamna Okezie Ikpeazu ya bar ƙaramar hukumar Bende inda aka yi bikin karrama tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bende, Hon. Nnenna Ukeje.
Ukeje ya shafe kimanin shekaru 12 a majalisar wakilai na tarayya.
KU KARANTA: An Yi Rige-Rigen Jefar Da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya
Harin ofishin ƴan sandan na Bende na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun ƙona ofishin yan sanda da ke kasuwar Ubani a ƙaramar hukumar Bende.
Ana zargin mambobin haramtacciyar kungiyar Independent People of Biafra, IPOB, ne suke kai harin duk da cewa sun musunta hakan.
A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.
Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.
Asali: Legit.ng