Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf

Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf

- Sanata Yusuf Abubakar Yusuf mai wakiltar jihar Taraba ya ce baya goyon bayan masu cewa Buhari ya yi murabus ko a tsige shi

- Ɗan majalisar ya ce ba shugaban ƙasa bane kawai nauyin samar da tsaro ya rataya a kansa kuma idan an tsige shi ma ƴan jam'iyyarsa ne za su cigaba da mulki

- Abubakar Yusuf ya ce Shugaba Buhari na iya kokarinsa kuma ya kamata yan kasa su bada gudunmawarsu tare da goyon bayansa

Shugaban kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawa, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf (APC, Taraba) ya soki wanda ke kira Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus ko a tsige shi saboda tsaro.

Ɗan majalisar, a hirar da ya yi da manema labarai a Abuja ya ce tsige Buhari ba zai magance matsalar tsaro a kasar ba, rahoton Daily Trust.

Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf
Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf. Hoto: @daily_trust

DUBA WANNAN: An Yi Rige-Rigen Jefar Da Gumakan Bauta Akan Sun Gaza Dakatar Da Annobar Korona a Indiya

Yusuf ya ce ba shugaban ƙasa kaɗai bane nauyin samar da tsaro ya rataya a kansa yana mai cewa gwamnoni da ƙananan hukumomi suma hakkin na kansu.

Ya ce, "Watanni kaɗan da suka gabata muna ta cewa shugaban kasa ya canja shugabannin tsaro, an canja su, mene ya canja?

"Wasu na cewa a raba kasar, wasu na cewa a canja shugaban kasa, ta yaya hakan zai taimake mu?

"Idan ka tsige shugaban ƙasa, wane zai maye gurbinsa? Ba mataimakinsa bane? Duk dai ba gwamnati ɗaya bane? Idan ka tsige shugaban ƙasa da mataimakinsa sai shugaban majalisa ya kama mulki, duk ba gwamnati ɗaya bane?

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kashe Ɗan Sanda a Zamfara Bayan Cacar-Baki Kan Cin Abinci Yayin Azumin Ramadan

"Ya zama dole muyi wani tunanin daban mu dauka cewa hakkin mu ne magance matsalar tsaro a ƙasar."

Don haka, Yusuf ya bukaci yan Nigeria su gane cewa ba aikin gwamnati kadai bane magance matsalar tsaro.

Sanatan ya ce a ganinsa Buhari na iya ƙoƙarinsa don haka ya kamata mu taimaka masa.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164