Labari Da Ɗuminsa: An Ga Wata a Nijar, Gobe Laraba Ne Sallah

Labari Da Ɗuminsa: An Ga Wata a Nijar, Gobe Laraba Ne Sallah

- An ga jaririn wata Shawwal a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Nigeria

- Ouhoumoudou Mahamadou, farai ministan kasar ne ya bada sanarwar a ranar Talata

- Mahamadou, cikin sanarwarsa ya ce an ga watan a yankuna uku a kasar don haka ranar Alhamis ne sallah

Wannan na zuwa bayan Najeriya, makwabciyar Nijar ta sanar da cewa ba a ga watan ba tare da ayyana Alhamis a matsayin ranar Sallah.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa an ga jaririn watan Shawwal hakan na nufin an kawo karshen watan azumin Ramadan na bana a kasar.

Labari da duminsa: An Ga Wata, Gobe Laraba Ne Sallah a Nijar
Labari da duminsa: An Ga Wata, Gobe Laraba Ne Sallah a Nijar
Asali: Original

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

Farai ministan kasar Ouhoumoudou Mahamadou ne ya tabbatar da ganin wata cikin sanarwar ta da ya fitar kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Kazalika, cikin sanarwar da ya fitar domin yan kasar ya ce an ga watan na Shawwal a wurare uku a kasar ta Nijar.

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

Amma a kasar Nigeria da ke makwabtaka da Nijar, Sarkin Musulmi Mai Alfarma Alhai Sa'ad Abubakar ya sanar da cewa ba a ga wata ba don haka za a cika azumi 30.

Don haka Sarkin Musulmin ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Nigeria murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

Sanar da Legit.ng Hausa ta gano a shafin kwamitin na Tuwita ya karanta: "Babu alamar ganin watan Shawwal a Nigeria yau Talata 11 ga Mayu, gobe Laraba 12 ga Mayu shi ne 30 ga Ramadan.

Nan gaba kadan za a fitar da wata sanarwa a hukumance daga majalisar.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel