Yan IPOB sun kashe mana yan sanda 21 a jihar Akwa Ibom, Kwamishanan yan sanda

Yan IPOB sun kashe mana yan sanda 21 a jihar Akwa Ibom, Kwamishanan yan sanda

- Yan kungiyar IPOB/ESN sun hallaka jami'an yan sanda da dama a kudu maso gabas

- Yanzu yan ta'addan sun fara kai hari ofishoshin yan sanda a kudu maso kudu

- A karshen makon da ya gabata, an kashe akalla yan sanda 7 a jihar Rivers

Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta ce tayi rashin akalla jami'a 21, ta yi rashin motoci 9 da kuma bindigogi 11 a hare-haren da yan ta'addan rajin kafa kasar Biyafara IPOB ke kaiwa.

Kwamishanan yan sanda, Amiengheme Andrew, ya bayyana hakan lokacin da gwamnan jihar, Udom Emmanuel da kwamishanoninsa suka kai mai ziyarar jaje hedkwatar hukumar, rahoton Vanguard.

Kwamishanan ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyara kuma yace wannan zai kara musu gwiwa.

Gwamnan ya shawarci jami'an yan sandan kada su karaya da abubuwan dake faruwa, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar na tare da su.

Gwamnan yace, "Ina jajantawa hukumar bisa rashin hafsoshinsu da makamansu sakamakon matsalar tsaron da ake fuskanta a jihar."

Ya kara da cewa ya kai wannan ziyara ne domin nuna alhininsa game da abubuwan da suka faru, inda ya jaddada cewa rayuwar dan sanda na da muhimmanci garesa.

DUBA NAN: Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya

Yan IPOB sun kashe mana yan sanda 21a jihar Akwa Ibom, Kwamishanan yan sanda
Yan IPOB sun kashe mana yan sanda 21a jihar Akwa Ibom, Kwamishanan yan sanda Hoto: The Nigerian Police Force
Asali: UGC

DUBA NAN: Bayan shekaru 35 tana aikin shara banki, ta ajiye aikin amma ta bar wasika mai sosa zuciya

A bangare guda, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya bada kyautar 20 miliyan ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami'an yan sanda 11 da aka kashe a hare-haren da yan bindiga suka kai musu a faɗin jihar.

Gwamnan, wanda ya sanar da haka yayin da yakai ziyarar ta'aziyya ga kwamishinan yan sandan jihar, Friday Eboka, a hedkwatar hukumar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Lokacin da yake jawabi ga jami'an yan sandan a Patakwal, gwamna Wike yace ya kawo musu ziyara ne domin ya jajanta musu bisa rashin wasu daga cikin abokan aikinsu, waɗanda suka rasa rayuwansu a ƙoƙarin kare jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel