Wike Ya Bada Kyautar Miliyan N220m Ga iyalan Jami'an Yan Sanda 11 da Aka Kashe
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bada gudummuwar miliyan 20 ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami'an yan sanda 11
- Gwamnan yace babu wani kuɗi da zai iya maye gurbin ran ɗan adam
- Kwamishinan yan Sandan jihar, Friday Eboka, ya yabawa gwamnan bisa wannan kulawa
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya bada kyautar 20 miliyan ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami'an yan sanda 11 da aka kashe a hare-haren da yan bindiga suka kai musu a faɗin jihar.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA
Gwamnan, wanda ya sanar da haka yayin da yakai ziyarar ta'aziyya ga kwamishinan yan sandan jihar, Friday Eboka, a hedkwatar hukumar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Lokacin da yake jawabi ga jami'an yan sandan a Patakwal, gwamna Wike yace ya kawo musu ziyara ne domin ya jajanta musu bisa rashin wasu daga cikin abokan aikinsu, waɗanda suka rasa rayuwansu a ƙoƙarin kare jihar.
Gwamnan ya ƙara da cewa duk da babu wasu kuɗi da zasu yi dai-dai da ran mutum, amma tallafin gwamnatin jihar zai tabbatarwa iyalan mamatan cewa yan uwansu basu mutu hakanan ba.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina
Yace: "A makwanni biyu zuwa uku da suka gabata, mun rasa jami'an yan sanda 11, wannan lokaci ne mai muni a wajen mu."
"Waɗanda ke wannan ɗanyen aikin sun mayar da matan jami'an zawarawa, yayin da suka maida yayan su marayu, ba tare da wani dalili ba."
A nasa ɓangaren, kwamishinan yan sandan jihar, amadadin muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba, ya yabawa gwamnan bisa nuna kulawarsa ga iyalan jami'an da suka rasu.
A wani labarin kuma Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe
Musulmi na farko da ya taɓa lashe zaɓen magajin garin Landan, Sadiq Khan, ya sake komawa kan kujerar sa a karo na biyu bayan kammala Zaɓe
Khan ya sake samun nasara ƙarƙashin jam'iyyar hamayya ta Labour da kashi 55.2% yayin da babban abokin takararsa keda kashi 44.8%.
Asali: Legit.ng