Bayan shekaru 35 tana aikin shara banki, ta ajiye aikin amma ta bar wasika mai sosa zuciya

Bayan shekaru 35 tana aikin shara banki, ta ajiye aikin amma ta bar wasika mai sosa zuciya

- Wata mata mai suna Julie kwanakin nan ta ajiye aikinta a banki bayan shekaru 35

- Amma Julie bata tafi haka kawai ba, ta ajiye wasika mai sosa zuciya ga shugaban bankin mara mutunci

- Mutane a kafafen sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu kan abinda ke cikin wasikar da ta rubuta

Wata mata mai aikin shara a banki ta ajiye aikinta bayan shekaru 35 tana gwagwarmaya don ciyar da yaranta.

Matar mai suna Julie, ta bar wasika mai sosa zuciya ga Manajan kuma hakan ya sanya mutane magana a kafafen sada zumunta.

'Danta mai suna @joecousin89 a Twitter, ya bayyana wasikar inda ya taya mahaifiyarsa murnar ajiye aikin kuma Allah zai saka mata bisa abinda Manajan yayi mata na zaginta gaban jama'a.

Yace: "Ga dalilin da yasa nike son mahaifiyata. Shekaranta 35 tana shara a bankuna amma yau ta ajiye aikin tare da ajiye wasikar ga Manajan mara mutunci."

A wasikar, mahaifiyar yaron ta caccaki Manajan kan abinda yake mata na wulakanci.

Wasikar yace: "Gobe zan daina aikin shara ga HSBC... Na jiye aikin bayan yadda ku kayi min tatas a ofis....Daga yanzu ku tuna cewa a rayuwar nan mutum ya kasance mai kirki saboda babu wanda yafi mai shara cikinku."

KU DUBA: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

Bayan shekaru 35 tana aikin shara banki, ta ajiye aikin amma ta bar wasika mai sosa zuciya
Bayan shekaru 35 tana aikin shara banki, ta ajiye aikin amma ta bar wasika mai sosa zuciya Hoto: @joecousin
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ba zamu yarda Bayarabe wanda ba Musulmi ba ya zama shugaban kasa, MURIC

A bangare guda, SpaceX, wani kamfanin Amurka da ke hada tauraron dan Adam wanda hamshakin attijirin nan, Elon Musk ya samar, yana neman sahalewar hukuma don fara samar da intanet dinsa mai suna Starlink a Najeriya.

Wakilan kasuwancin Afirka na SpaceX, Ryan Goodnight ne ya bayyana haka, yayin wata tattaunawa da shugaban hukumar sadarwa ta kasa (NCC), Farfesa Umar Danbatta, a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel