Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya

Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya

- Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, na zargin rundunar sojin ƙasar nan da shiryawa yankin kudu-gabas da kudu-kudu wata maƙarƙashiya

- Ƙungiyar tace sojin na tura kwamandoji yan arewa zuwa yankin domin tada hankulan matasan yankin

- Rundunar soji ta musanta wannan zargin inda tace tsarin tura jami'ai zuwa wasu yankuna baya duba addini, ƙabila, al'ada ko kuma yankin da mutum ya fito

Rundunar sojin ƙasar nan da ƙungiyar inyamurai, Ohanaeze Ndigbo, sun saɓa wa juna bisa zargin tura kwamandoji yan arewa zuwa yankin kudu maso gabas da kuma kudu maso kudu na ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina

Yayin da ƙungiyar ta nuna rashin amincewarta ga dokar 'Duk wanda aka kama da makami a harbeshi' da gwamnati ta bawa soji.

Ohanaeze ta gargaɗi gwamnatin Najeriya da ta koyi darasi a tarihin baya, kada tayi yaƙin da ba zata sami nasara ba a kan yan ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma shawarci gwamnatin shugaban ƙasa Buhari "ta duba hanyoyin kawo zaman lafiya" hakan kaɗai ne zai tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma samar da zaman lafiya.

Hakanan kuma, rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake mata, kuma ta ƙara jaddada cewa tura jami'an tsaro zuwa wasu yankuna wani aiki ne na yau da kullum kuma ana yinsa ne bisa duba kwarewar jami'an.

Rundunar ta ƙara da cewa bata bada horo, ko tura wani jami'i bisa duba banbancin addini, al'ada, yare ko kuma yankunan ƙasar nan.

Amma a wani jawabi da ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta fitar ta hannun kakakin ƙungiyar, Alex Ogbonnia, jawabin yace:

"An jawo hankalin mu bisa tsarin da jami'an soji suke bi wajen tura jami'ai yan arewa zuwa yankin kudu maso gabas wanda hakan yasa ake samun rahoton kashe-kashe a yankin."

"A wani rahoto da aka buga a yanar gizo ya bayyana cewa a shirin da ake na duk wanda aka kama da makami a sheke shi, rundunar soji ta tura musulmai yan arewa a matsayin waɗanda zasu jagoranci aikinta a jihohin Anambra, Imo, Abia, Akwa Ibom, Enugu, Benue, Edo, Delta da kuma Rivers."

"A jihar Anambra, kwamandan bataliya ta 302 dake Onitsha, Shine Abdulsalam Abubakar Sambo wanda bahaushe ne kuma musulmi, Yayin da a jihar Imo Kwamandan birged ta 34 shine Janar Ibrahim Tukura, wanda shima ɗan arewa ne.

KARANTA ANAN: Wike Ya Bada Kyautar Miliyan N220m Ga iyalan Jami'an Yan Sanda 11 da Aka Kashe

Jawabin ya cigaba da cewa:

"A jihar Abia, kwamandan birged ta 14 dake Ohafia, Janar M. Ibrahim shima dai ɗan arewa ne, yayin da a jihar Akwa Ibom, kwamandan birged ta 2 dake Uyo, Janar Faruk Mijinyawa, shima wani ɗan arewa ne. Wannan babban abun damuwa ne."

"Dokar duk wanda aka kama da makami a harbeshi da aka baiwa jami'an soji a kan matasan mu a mako mai zuwa abun damuwa ne. Rahoton duk shirye-shiryen su ya fito fili, kuma an bayyana cewa zasu fara wannan aikin ne daga Orlu a jihar Imo."

"Shugaban ƙungiyar mu, George Obiozor, yana kira ga gwamnatin Najeriya data koyi darasi a tarihin baya, domin kada ta fara yaƙin da ba zata samu nasara ba, amma ta duba yuwuwar hanyoyin sulhu waɗanda sune kaɗai zasu tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma kawo zaman lafiya."

A wani labarin kuma Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Hukumar binciken sararin sama ta ƙasa NASRDA tayi hasashen cewa jinjirin watan shawwal ba zai bayyana ba sai ranar Laraba 12 ga watan Mayu.

Hukumar tace idan har hasashen ta ya zama gaskiya, musulmai zasu gudanar da sallar Eid Fitr a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel