Elon Musk Zai Kafa Kamfanin Sadarwar Ta Intanet a Nigeria

Elon Musk Zai Kafa Kamfanin Sadarwar Ta Intanet a Nigeria

- Za a kafa tauraron dan Adam na kamfanin SpaceX nan ba da dadewa ba a Najeriya

- Wakilin Africa na kamfanin SpaceX mallakar Elon Musk ne ya bayyana haka a satin da ya gabata

- Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da shugaban hukumar NCC Farfesa Umar Danbatta

SpaceX, wani kamfanin Amurka da ke hada tauraron dan Adam wanda hamshakin attijirin nan, Elon Musk ya samar, yana neman sahalewar hukuma don fara samar da intanet dinsa mai suna Starlink a Najeriya.

Wakilan kasuwancin Afirka na SpaceX, Ryan Goodnight ne ya bayyana haka, yayin wata tattaunawa da shugaban hukumar sadarwa ta kasa (NCC), Farfesa Umar Danbatta, a Abuja, The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona

Elon Musk Zai Kafa Kamfanin Sadarwar Ta Intanet a Nigeria
Elon Musk Zai Kafa Kamfanin Sadarwar Ta Intanet a Nigeria. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

A cewar Goodnight, Najeriya na daga cikin manyan cibiyar kasuwancin Afirka. Kafin tattaunawar gani da idon da akq gudanar satin da ya gabata, SpaceX ta tattauna sau da dama ta yanar gizo a watannin da suka gabata.

Danbatta, wanda ya samu wakilcin Ubale Maska, kwamishinan ayyukan fasaha na hukumar, ya ce hukumar zata yi duk abin da ya dace don ganin an tabbatar da samar da sababbin fasaha.

Ya bayyana cewa hukumar na da sha'awar samar da nagartattun hanyoyin sadarwa ga kauyuka, ta hanyar cimma abun da aka yi tanadi na NNBP, 2020-2025.

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

Da yunkurin gwamnati na dawo da kashi 90 cikin yan kasa kan yanar gizo zuwa nan 2025, za a gudanar da abubuwa da dama don tabbatar da wannan.

Wani rahoto da aka fitar a watan Mayu 2021 mai taken "Space in Africa" ya bayyana cewa an shirya kafa tauraron dan Adam din a Najeriya, sai kuma sauran kasashen Africa daga baya.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel