Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

- Da alamun azumi 30 Musulmai zasu yi bana yayinda kwamitin duban wata tace ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba

- Ranar Talata aka bada umurnin duba watan duk da haka

Kwamitin duban wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya ta sanar da cewa ganin jinjirin watan Shawwal ranar Talata, 29 ga watan Ramadana da kamar wuya.

A bayanin da kwamitin tayi ranar Asabar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an yi hasashen ko wata ya bayyana zai fito ne gabanin faduwar rana, saboda haka ba zai yiwu a ga jinjirin wata ranar Talata a Najeriya ba.

Amma duk da haka jama'ar Musulmi a fadin Najeriya su fita neman jinjirin wata saboda yin hakan ibada ne.

Ranar Talata, 11 ga Mayu ya yi daidai da 29 ga watan Ramadana da ake fara neman jinjirin watan Shawwal na shekarar 1442AH.

DUBA NAN: Da yiwuwan rokan China da ya bace a sararin samaniya ya fadi a Abuja

Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata
Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata Hoto: NMSC of NSCIA
Asali: Facebook

DUBA NAN: Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

Wani sashen jawabin yace: "A ranar Talata, 29 ga Ramadana 1442AH (11 ga Mayu, 2021).. Tun da haihuwar jinjirin ba zai faru ba kuma wata zai fadi gabanin rana, hakan na nuna cewa ba zai yiwu a ga wata a Najeriya ranar Talata 11 ga Mayu, 2021 ba.

"Amma dai a sani cewa neman wata kowace ranar 29 ga wata ibada ne."

"Saboda haka a nemi wata ranar Talata."

Kwamitin ta kara da cewa duk wanda yayi ikirarin ganin wata, wajibi ne ya bada gamsasshen bayanin yadda ya gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel