Ba zamu yarda Bayarabe wanda ba Musulmi ba ya zama shugaban kasa, MURIC
- Kungiyar MURIC ta caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
- Shugaban MURIC ya ce an dade ana rainawa Musulmai yan kabilan Yoruba wayo
- Ana kyautata zaton jigon APC Asiwaju Ahmed Tinubu zai yi takara a 2023
Kungiyar kare hakkin Musulmai watau MURIC ta bayyana cewa ba zai yiwu a baiwa wani dan kabilan Yoruba tikitin takarar shugaban kasa ba idan ba Musulmi bane.
A jawabin da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya sake ranar Litinin, ya bayyana cewa tsohon shugaba Obasanjo na kokarin shigo da shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina, cikin takarar kujeran shugaba a 2023.
A cewarsa, kokarin sanya Adesina wanda Bayarabe Kirista ne cikin takaran rashin adalci ne da daidaito.
Ya kara da cewa Yarabawa Kiristoci uku sun yi mulkin Najeriya amma babu Bayarabe Musulmi ko guda da ya taba rike kujeran shugaban kasa ko mataimaki.
DUBA NAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun
KU KARANTA: Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallah a bana
"Wannan wani kokari ne na hana Musulmai Yarabawa kujerar shugaban kasa. Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo na kokarin shigar da shugaban bankin AfDB cikin takarar shugaban kasan 2023," Yace.
"Ba zamu yarba da hakan ba. Muna tunawa tsohon shugaban cewa a matsayinsa na bayarabe Kirista, ya mulki Najeriya sau biyu. Cif Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan ya yi shugaban rikon kwarya. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ma Bayarabe Kirista ne."
"Kowa ya sani cewa Musulmai Yarabawa sun fi yawa a kudu maso yamma amma ana hanasu hakkinsu."
Asali: Legit.ng