An kashe N25bn wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnan CBN

An kashe N25bn wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnan CBN

- A shekarar 2020, bayan gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu sun bada gudunmuwar kudade na raba tallafi ga talakawa

- Kamfanonin sun radawa kansu suna gamayyar yaki da Korona wato CACOVID

- Gwamnan CBN ya bayyana cewa CACOVID ta kashe kimanin N25bn

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yunkurin da kamfanoni masu zaman kansu sukayi na raba kayan tallafin Koronan bilyan 25 ya taimakawa talakawa sosai.

Punch ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne a shirin kaddamar da wani Fim mai suna 'Unmasked' ranar Juma'a a jihar Legas.

Emefiele, wanda ya samu wakilcin mukaddashin diraktan sadarwa na CBN, Osita Nwamsobi, ya bayyana cewa wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun hada cibiyoyin killace masu Korona 39 a fadin tarayya.

Yace, "Akan wannan mun bada bashin N83.9bn ga kamfanonin hada magani da Likitoci, kuma hakan na taimakawa wasu ayyukan bincike 26 da samar da magani 56 a fadin tarayya."

"Hakazalika mun samu nasarar janyo hankalin masu ruwa da tsaki a Najeriya ta gamayyar CACOVID, wanda hakan ya taimaka wajen samar da kayan tallafin N25bn ga gidajen da annobar ta shafa da kuma kafa cibiyoyin killace masu cutar guda 39 a fadin tarayya."

Wadannan kamfanoni da suka bada gudunmuwa sun hada da Dangote, BUA, bankin Access dss.

DUBA NAN: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

An kashe N25bn wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnan CBN
An kashe N25bn wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnan CBN Hoto: @cacovidng
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwananmu 56 ba wanka, Daliban Afaka 27 da suka samu kubuta

A bangare guda, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya lashi takobin cewa ba zasu sake yarda wani ya shigo da Masara daga kasar waje ba.

Emefiele ya bayyana hakan a bikin kaddamar da kakar noman Masara karkashin shirin bada rancen kudi da CBN ta shiryawa kungiyar manoma masara a Najeriya (MAAN).

A jawabin da bankin ya saki ranar Laraba, Gwamnan ya yi kira ga matasan Najeriya su rungumi aikin noma, inda ya tabbatar musu da cewa bankin shirya take da taimaka musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel