Kwananmu 56 ba wanka, Daliban Afaka 27 da suka samu kubuta

Kwananmu 56 ba wanka, Daliban Afaka 27 da suka samu kubuta

- Daliban Afaka sun bayyana irin halin da suka shiga kimanin watanni biyu da sukayi hannun yan bindiga

- Sun bayyana cewa sau daya suka ci Shinkafa da taliya

- A cewar matan, babu wanda yayi lalata da su kuma babu wanda aka kashe

An farke da farin ciki yayinda dalibai 27 na kwalejin fasahar gandun daji, FCFM Afaka, a jihar Kaduna suka gamu da iyayensu bayan kwanaki 56 cikin daji hannun yan bindiga.

Da misalin karfe 3 na ranar, dalibai da malami a makarantar sun shiga farin ciki lokacin da Kwamishanan yan sanda, Umar Muri, da kwamishanan tsaro, Samuel Aruwan, suka mika daliban hannun shugabannin makarantar.

A cewar Punch, wata daliba cikin wadanda aka sace, Sarah Sunday, ta ce sun shiga wani irin mugun hali, inda ko wanka ba'a amince musu sun yi ba.

Sarah tace, "Abubuwa da yawa sun faru da mu a wajen. Mun sha yunwa. Mun yi tattaki da wahala. Mun sha zagi amma mungode basu yi lalata da kowa ko kashe wani cikinmu ba. Ranar farko kadai suka bugemu lokacin da suka bidiyonmu."

Yayinda aka tambayeta abincin da suka ci, Sarah tace, " Mazajen ke zuwa debo mana ruwa don girki. Muna girka tuwo da miyan kuka, da kuma miyan kubewa. Sau daya muka girka shinkafa, kuma mun dafa taliya sau daya."

KU KARANTA: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

Kwananmu 56 ba wanka, Daliban Afaka 27 da suka samu kubuta
Kwananmu 56 ba wanka, Daliban Afaka 27 da suka samu kubuta
Asali: Twitter

DUBA NAN: Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

Sarah Sunday ta kara da cewa sun yafewa waɗanda suka sace su, The Cable ta ruwaito.

An sace ɗaliban ne a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a makarantarsu a ranar 12 ga watan Maris na 2021.

Gwamnatin jihar Kaduna ta garzaya da ɗaliban zuwa asibiti ne domin a duba lafiyarsu kafin daga bisani a yau Juma'a aka sada su da iyalansu.

"Zan fada musu (tana nufin masu garkuwar) cewa dukkanin mu mun yafe musu. Shi ke nan. Wannan shine kaɗai abin da zan faɗa musu. Kuma Allah zai ba su ikon su canja halayensu," in ji ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel