Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN

Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN

- Najeriya na da isasshen masara da zai isa dukkan abinda ake so, cewar Emefiele

- A cewarsa, akwai akalla buhuhunan Masara 50,000 a wajen taron

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya lashi takobin cewa ba zasu sake yarda wani ya shigo da Masara daga kasar waje ba.

Emefiele ya bayyana hakan a bikin kaddamar da kakar noman Masara karkashin shirin bada rancen kudi da CBN ta shiryawa kungiyar manoma masara a Najeriya (MAAN).

A jawabin da bankin ya saki ranar Laraba, Gwamnan ya yi kira ga matasan Najeriya su rungumi aikin noma, inda ya tabbatar musu da cewa bankin shirya take da taimaka musu

Ya ce CBN ba za ta lamunci cigaba da shigo da Masara daga kasashen waje ba, inda ya bayyana cewa Manoma Masara a Najeriya na da ikon samarwa yan Najeriya ton milyan 4.5 da ake bukata a kasar.

"Da buhuhunan Masara sama da 50,000 a kasa, da kuma wasu a wurare daban-daban, manoma masara na bayyanawa jama'a cewa zamu iya noma Masarar da muke bukata a kasar nan," yace.

KU KARANTA: Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar

Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN
Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin shugabannin kasa 15 mafi yawan albashi a nahiyar Afrika, ciki akwai Buhari

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa manoma masara cewa gwamnati za ta cigaba da taimaka musu don tabbatar da cewa sun yi aikinsu yadda ya kamata.

A bangare guda, Ministar kuɗi, Zainab Ahmed, ta musanta zargin dake cewa gwamnatin tarayya na shirye-shiryen zabtare albashin ma'aikatu, da hukumomin gwamnati.

A wani jawabi da mai baiwa ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Yunusa Tanko-Abdullahi, ya fitar, Mrs. Ahmed tace gwamnati bata da niyyar zabtare alabashin ma'aikata sai dai tana shirin gudanar da dai-daito a tsakanin ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel