Gwamnatin tarayya ta saki kimanin bilyan 30 don sayan rigakafin Korona

Gwamnatin tarayya ta saki kimanin bilyan 30 don sayan rigakafin Korona

- Ministar kudi ta bayyana kokarin da Najeriya keyi don tabbatar da cewa kowa ya samu rigakafin Korona

- Bayan samun kyautar rigakafin Astrazanece, Najeriya na shirin siyaan ta Johnson&Johnson

- Ana shirin yiwa kashi 70 cikin 100 na yan Najeriya rigakafi nan da shekarar 2022

Gwamnatin tarayya ta ce ta baiwa hukumar inganta lafiya na farko wato NPHCDA kudi bilyan 29.1 don sayowa yan Najeriya rigakafin cutar Korona.

Ministar kudi, da kasafinsa, Zainab Ahmad Shamsuna ta bayyana hakan ne a taron gangamin yanar gizo kan inganta kasafin kudi a nahiyar Afrika CABRI, ranar Juma'a, rahoton Daily Nigerian.

A cewar Ministar, gwamnatin tarayya za ta sayi rigakafi Johnson & Johnson guda milyan 29.588 ta hannun AFREXIMBank.

Zainab ta ce gwamnati na kokarin gabatar da sabon kasafin kudi ga majalisa don a kara kan kasafin kudin 2021 don sayan wannan rigakafin.

"Karin kasafin kudin don sayan rigakafin COVID-19 zai hada da kudin sayan rigakafin, kudin kawosu Najeriya, da kuma kudin sufurinsu yayin rabawa jihohi," tace.

"Ma'aikatar lafiya na shirin yiwa kashi 70 na yan Najeriya (masu shekaru 18 da abinda yayi sama) tsakanin 2021 da 2022."

Ta bayyana cewa Najeriya ta samu isasshen rigakafin Korona na gudunmuwa daga COVAX wanda zai iya yiwa mutum milyan 43.1.

KU KARANTA: Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

Gwamnatin tarayya ta saki kimanin bilyan 30 don sayan rigakafin Korona
Gwamnatin tarayya ta saki kimanin bilyan 30 don sayan rigakafin Korona Credit: Presidency
Asali: Facebook

DUBA NAN: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

A bangare guda, kungiyar dake kare haƙƙin ƙananan yara, UNICEF, ta roƙi yan Najeriya waɗanda aka yi ma rigakafin COVID19 ta AstraZeneca a karon farko da su koma a sake yi musu ita a karo na biyu.

Ƙungiyar dake taimaka ma yara da kuma ɗalibai,UNICEF, ta ce sake yin allurar zai ƙara ma kwayoyin halittar jikin mutum ƙarfi su yaƙi cutar yadda ya kamata.

Elizabeth Onitolo, wanda ta ƙware kan harkar sadarwa domin kawo cigaba a UNICEF, ita ce ta yi wannna kiran ranar Laraba a Yola a wurin taron kwana uku akan allurar rigakafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel