UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu

UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu

- UNICEF ta roƙi yan Najeriya waɗanda aka yiwa allurar rigakafin korona da su sake komawa a tsira musu allurar a karo na biyu

- A cewar UNICEF ɗin hakan zai ƙara ma ƙwayoyin halittar jikin mutum ƙarfi sosai wajen yaƙar cutar

- Ƙungiyar ta faɗi haka ne a wajen taron ƙarama ma juna sani na kwana uku da data shirya tare da haɗin gwiuwar ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu ta ƙasa

Ƙungiyar dake kare haƙƙin ƙananan yara, UNICEF, ta roƙi yan Najeriya waɗanda aka yi ma rigakafin COVID19 ta AstraZeneca a karon farko da su koma a sake yi musu ita a karo na biyu.

KARANTA ANAN: Bayan ta kafa tarihin fita da sakamako mafi kyau a jami'a, yar Nageriya ta samu tallafin zuwa Amurka

Ƙungiyar dake taimaka ma yara da kuma ɗalibai,UNICEF, ta ce sake yin allurar zai ƙara ma kwayoyin halittar jikin mutum ƙarfi su yaƙi cutar yadda ya kamata.

Elizabeth Onitolo, wanda ta ƙware kan harkar sadarwa domin kawo cigaba a UNICEF, ita ce ta yi wannna kiran ranar Laraba a Yola a wurin taron kwana uku akan allurar rigakafi.

Ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu ta ƙasa ta shirya taron da haɗin gwuiwar UNICEF kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu
UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu Hoto: @UNICEF_Nigeria
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Sun sheƙe wasu yan fashin teku 4 a jihar Akwa Ibom

Mrs Onitolo ta roƙi waɗanda suka yi allurar a baya da su cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar saboda su kare waɗanda suke rayuwa da su tare.

Ta ce akwai bukatar mutane suje a yi musu rigakafin sannan kuma su cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar.

Hakanan kuma, Lilian Okeke, shugabar tawagar ƙungiyar AFENET a jihar Adamawa, ta ce an samar da rigakafin ne domin kare rayuwar mutane.

"Buƙatar mu ita ce mu kare rayukanku, saboda haka ku cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar don kare kanku." inji Okeke.

Ta kuma baiwa mata masu ɗauke da juna biyu da su tuntuɓi likitoci kafin suje ayi musu irin wannan allurar rigakafin ta COVID19.

A wani labarin kuma APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa saboda zuwan Ramadana

Jami'iyyar APC ta raba kayan abinci cike da manyan motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa da mabuƙata a jihar Zamfara.

Tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari ne ya bayyana haka a Gusau, babban birnin jihar, lokacin da jam'iyyar ta ƙaddamar da fara rabon kayan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel