Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

An dakatad da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa a Najeriya NPA, Hadiza Bala Usman, domin bada dama don gudanar da bincike kan wasu kudaden da ake zargin ba'a sanya a asusun bai daya ba.

Wasu takardu da Legit Hausa ta gani sun nuna yadda Ministan Sufuri yayi zargin badakalar N165bn.

A bisa wasikar da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya aikewa shugaba Buhari, ya ce adadin kudaden ya kamata ace hukumar NPA ta tura asusun gwamnatin tarayya tsakanin 2016 da 2020 basu kai ba.

A wasikar mai ranar wata, 4 ga Maris, 2021, Amaechi ya bayyana cewa a wadannan shekarun, NPA bata shigar da kudi N165 billion ba.

Saboda haka, Amaechi ya bada shawara a gudanar da bincike kan asusun NPA.

Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman
Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman
Asali: Facebook

Martani kan haka, Hadiza Bala Usman a ranar 5 ga Mayu ta aike wasika fadar shugaban kasa inda ta bayyana cewa lissafin da ofishin kasafin kudi tayi na zargin rashin shigar da kudi akwai kura-kurai kuma ya sabawa dokar Fiscal Responsibility Act.

Ya ce lissafin da ofishin kasafin kudi tayi na rarar kudin 2017 da 2018 ya wuce abinda lissafin da NPA tayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng