Ana cikin azumi, ‘Yan bindiga sun shiga Kauye, sun buda wuta, sun kashe Bayin Allah

Ana cikin azumi, ‘Yan bindiga sun shiga Kauye, sun buda wuta, sun kashe Bayin Allah

- Miyagun ‘Yan bindiga sun kuma aukawa wani Kauye a cikin jihar Neja

- Wannan karo an hallaka mutane bakwai a karamar hukumar Magama

- ‘Yan bindigan sun dura garin Yangalu dauke da makamai a kan babura

Mutane bakwai ake zargin sun mutu yayin da wasu ‘yan bindiga su ka kai hari a kauyen Yangalu, karamar hukumar Magama da ke jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan bindiga birjik su ka auka wa mutanen Yangalu, inda su ka rika buda wuta, suna harbi ta ko ina.

Kamar yadda mu samu labari dazu, wadannan miyagu da su ka zo dauke da bindiga sun tada hankalin jama’a da suka shiga harba bindigogi.

KU KARANTA: Buhari ya fito ya yi mana magana - Dino Melaye

A ‘yan kwanakin nan, irin wadannan munanan hare-hare suna neman zama ruwan dare a jihar Neja.

‘Yan bindigan sun goya junansu a kan babura, suna rike da bindigogi. A haka suka shiga kauyen, su ka yi barnarsu, ba tare da an kawo wani dauki ba.

Rahotanni sun bayyana a halin yanzu, ‘yan bindiga sun yi ta’adi a kauyuka kusan 70. Hakan ya jikkata Bayin Allah da-dama, sannan an kashe wasu.

Kafin ‘yan bindigan su fita daga kauyen Yangalu, sai da suka tabbata sun yi wa al’umma barna, suka jawo wa mutane asara, aka zubar da kayan abinci.

KU KARANTA: Bikin Sallah: An haramta hawa dawaki a jihar Neja

Ana cikin azumi, ‘Yan bindiga sun shiga Kauye, sun buda wuta, sun kashe Bayin Allah
Sufetan 'Yan Sanda na kasa Hoto: Facebook/ngpolice
Asali: Facebook

Shugaban karamar hukumar Magama, Alhaji Sufiyanu Yahaya, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, kuma har ya taka kafarsa ya ziyarci kauyen.

Da ya je yi wa al’ummar Yangalu jaje, Sufiyanu Yahaya, ya sha alwashin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin a inganta tsaron yankin.

Sanatan jihar Borno, Ali Mohammed Ndume, ya bayyana yadda harkar ta jagwalgwale a Najeriya, inda aka gaza kawo karshen 'Yan Boko Haram har yau.

‘Dan Majalisar ya ce bai taba ganin Sojan kasar nan dauke da sabuwar AK-47 ba. A cewarsa, an koma ana raba wa sojoji harsashin da za su yi aiki da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel