Da Ɗumi-Ɗumi: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger

Da Ɗumi-Ɗumi: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger

- Gwamnatin jihar Niger ta hana hawa dawakai a unguwanni da kuma yayin bukukuwa a jihar

- Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya ce an dauki matakin ne bayan ƙorafi da aka daɗe ana yi

- Ibrahim Matane ya ce iyaye da masu dawakai su gargadi ƴaransu domin duk wanda aka kama yana saɓa dokar zai fuskanci hukunci

Gwamnatin jihar Niger ta haramta hawan dawakai na gargajiya da kuma yayin bukukuwa da shagulgula a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, SSG, Ahmed Ibrahim Matane ne ya sanar da hakan yana mai cewa an dauki matakin ne sakamakon ƙorafin da dama da aka shigar na cewa wasu na fakewa da hawan dawakai suna aikata miyagun ayyuka.

Da Ɗumi-Ɗumi: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger
Da Ɗumi-Ɗumi: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

Matane ya yi kira ga dukkan mutanen da ke jihar su yi biyayya ga umurnin yana mai gargadi cewa gwamnati ba za ta lamunci saɓa doka ba.

Ya yi kira ga masu dawakai da iyaye su gargadi ƴaransu, ya kara da cewa duk wanda aka kama yana hawan doki, za a ƙwace dokin a kuma hukunta shi.

Ya ce, "Gwamnati mai ci yanzu ba za ta zuba ido tana kallo wasu marasa tarbiyya suna aikata laifuka a jihar ba.

"Gwamnati ba za ta amince da duk wani abu da ka iya zama barazana ga tsaro ba don haka za ta magance lamarin."

KU KARANTA: Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto

Har wa yau, SSG ɗin ya gargadi masu amfani da dandalin sada zumunta su guji yaɗa labaran ƙarya da ka iya tsorata mutane, yana mai cewa gwamnati ba za ta ƙyalle su ba

Ya bawa mutane tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta magance dukkan mutanen da ke aikata laifuka a jihar ya kuma bukaci su cigaba da addu'a domin ganin jihar ta fita daga ƙangin rashin tsaro da ta shiga.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel