Abubuwa sun tabarbare yanzu, har ana kayyadewa Soji harsashin da zai rike inji Sanata
- Ali Mohammed Ndume ya koka a kan halin tsaron da ake ciki a kasar nan
- Sanatan Borno ta Kudu ya ce ana warewa sojoji kayan da za su yi aiki da su
Ali Mohammed Ndume, Sanata mai wakiltar mutanen Borno ta Kudu ya bayyana cewa abubuwa basu tafiya yadda su ka kamata a yakin Boko Haram.
Sanata Ali Mohammed Ndume ya ce lamarin har ya kai ana ware adadin harsashin da ake ba sojoji.
The Cable ta ce ‘dan majalisar ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a garin Abuja, inda ya yi kira ga hukuma su inganta halin da jami’an tsaro suke ciki.
KU KARANTA: Ana rade-radin Boko Haram za su kai hari a Majalisa
Jaridar ta rahoto Ali Mohammed Ndume ya na cewa sojoji sun saba da wannan tsari na kayyade masu yawan harsashin da za su fita zuwa filin daga da su.
“Ba a taba yin lokacin da abubuwa su ka tabarbare mana ta ko ina irin wannan lokaci ba. Lamarin ya lalace ta yadda an koma yin sulhu da ‘yan bindiga.”
“A Shiroro, mazauna gari sun yi sulhu da ‘yan bindiga, aka ba su damar su zauna lafiya. Yau a Najeriya, mu na da wasu masu iko a cikin gwamnatinmu.”
“Idan muka tunkari jami’an sojoji a kan ‘me yake hana ku aiki?’ sai su ce mana ‘ba mu da kudi’; muna lallaba abin da mu ka samu ne.” inji Sanata Ndume.
KU KARANTA: Tsohon Sanata ya zargi Gwamnan Ekiti da kokarin murkusa APC
“Ina magana da jami’an tsaro a kai-a kai. Abin ya kai inda ya kai, sojojin kasa suna kayyade harsashi. An saba wannan, a raba harsashin da za ayi aiki da su.”
“Za a iya cewa ni na fada.” Sanatan ya na mai bada tabbacin zancensa, ya ce: “Na zagaya dakarun sojoji; ban ga wani soja da sabuwar bindigar AK-47 ba har yau.”
A ranar Talata, shugaban kwamitin sojojin kasa a majaisar dattawa, Ali Muhammad Ndume, ya ja hankalin jama’a a kan halin da ake ciki a yakin Boko Haram.
Sanatan ya bayyana cewa ‘Yan Boko Haram na neman dawowa Borno da kewaye. ‘Dan Majalisar ya ce ka da ‘Yan ta’adda su hana a gina makaranta a garin Gwoza.
Asali: Legit.ng