Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba

Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba

- Tsohon sanata da ya taba wakiltar mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye yace 'yan Najeriya Buhari suka zaba

- Melaye ya bukaci Buhari da ya bude baki ya dinga yi wa 'yan Najeriya magana tunda ba Garba Shehu da Adesina suka zaba ba

- A cewarsa, matsalar tsaro na da nasaba da gazawar shugaban kasan, don haka yake kira gareshi da ya yayi murabus

Dino Melaye, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Kogi ta yamma, yace shugaban kasa Muhammadu koyaushe baya nan kuma bashi da lokaci.

Jigon jam'iyyar PDP yace ba zai yuwu shugaban kasan ya ki yi wa kowa magana ba sai ta bakin masu magana da yawunsa, TheCable ta wallafa.

Ya ce shirun Buhari na da matukar illa ga yaki da rashin tsaro a kasar nan. Melaye ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawar da aka yi da shi a AIT ranar Juma'a.

KU KARANTA: Tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke jami'ai 2 a Anambra

Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba
Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake kwashe daliban jami'a da ba a san yawansu ba

"Akwai bukatar shugaban kasa yayi magana kai tsaye da 'yan Najeriya, akwai bukatar yayi magana da kafafen yada labarai. Tamkar babu shugaban kasa kuma hakan yana da matukar illa ga yaki da ta'addanci a kasar nan," yace.

"Abun takaici ne. Babu abinda muke ji illa fadar shugaban kasa tace kaza da kaza. Ba mu zabi Garba Shehu da Adesina ba.

“Dukkan matsalar tsaronmu tana da tushe ne da rashin shugabanci nagari. Shugaban kasar Najeriya ya gaza, ba zai iya ba. Abinda nake tsammanin daga gareshi tunda ya nuna dukkan alamun gazawa na mulkin kasar nan.

"Shugaban kasa Buhari yayi murabus saboda 'yan Najeriya na mutuwa babu wani dalili."

A wani labari na daban, wata kungiyar karkashin inuwar #IstandwithBuhari# tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai saurari miyagun da ke kira gareshi ba da ya sauka mulki kafin cikan wa'adin mulkinsa a 2023.

A yayin jawabi ga manema labari a ranar Alhamis a cibiyar Yar'adua dake Abuja, shugaban kungiyar mai suna Ifeanyi Nonso, wanda ya samu goyon bayan sauran 'yan kungiyar, ya ce wasu 'yan siyasa ne a kasar nan ke daukar nauyin kashe-kashe.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce wasu 'yan siyasa ne a kasar nan ke zagon kasa ga kokarin gwamnati na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan inda ya kara da cewa nan babu dadewa asirinsu zai tonu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel