Jerin shugabannin kasa 15 mafi yawan albashi a nahiyar Afrika, ciki akwai Buhari
Kasancewarsu ma'aikatan gwamnati, shugabannin kasa a fadin duniya na karban albashi kamar kowani ma'aikacin gwamnati.
Bayan wannan albashi, shugabannin kasa na samun alawus daban-daban don jin dadinsu.
A cewar Answer Afrca, shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ne shugaban kasa a Afrika mafi yawan albashi.
Paul Biya ya fara mulkin kasar tun shekarar 1982.
KU KARANTA: Obasanjo Ga Buhari: Shawarwari 3 Kwarara Don Magance Matsalar 'Yan Bindiga
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DUBA NAN: Rawar da mahaifin kasurgumin dan bindiga ya taka wajen kubutar daliban Afaka 27
Ga jerin albashin da suke samu a shekara kamar yadda Africa Info 247 ya tattara :
1. Paul Biya, Kamaru - $620,976
2. Sarki Mohammed VI, Maroko - $488,604
3. Cyril Ramaphosa, Afrika ta kudu - $223,500
4. Uhuru Kenyatta, Kenya - $192,200
5. Yoweri Museveni, Uganda - $183,216
6. Abdelmadjid Tebboune, Algeria - $168,000
7. Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, Equatorial Guinea -$152,680
8. Emmerson Mnangagwa, Zimbabwe - $146,590
9. Denis Sassou, Jamhuriyyar Congo - $108,400
10. Alassane Ouattara, Ivory Coast - $100,000
11. George Weah, Liberia- $90,000
12. Paul Kagame, Rwanda -$85,000
13. Nana Akufo-Addo, Ghana - $76,000
14. Lazarus Chakwera, Malawi - $74,300
15. Muhammadu Buhari, Najeriya - $69,000
Yan Najeriya da dama sun bayyana mamakinsu kan yadda shugaban kasarsu, Muhammadu Buhari ya kasance mafi karancin albashi cikinsu.
Wasu da dama sun ce basu gamsu ba yayinda wasu suka ce zai fanshe a alawus.
Asali: Legit.ng