Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 74

Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 74

- Bayan shekara daya ana fafatawa a kotu, abin ya zo karshe

- Kotun Koli ta rraba gardama tsakanin INEC da jam'iyyun siyasa 74 da aka soke

- Kotun ta ce hukumar INEC na da karfin soke jam'iyyun siyasa a doka

Kotun kolin Najeriya a ranar Juma'a ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara inda aka amince da INEC ta soke jam'iyyar siyasa 74 saboda basu ci zabe ko guda ba.

A bara Legit ta kawo muku cewa, hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta soke jam'iyyun siyasa 74 a Najeriya.

Jam'iyyun da suka rage yanzu 16 ne kacal.

A zaman yanke hukuncin da Alkali Adamu Jauro ya jagoranta ranar Juma'a a Kotun Koli, ya ce soke jam'iyyar NUP da sauran jam'iyyu 73 daidai ne da kundin tsarin mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari

Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 74
Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 74
Asali: Original

DUBA NAN: Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa aka soke jam'iyyun. Dalilan sune:

1. Saba dokokin rijistan jam'iyyar siyasa a Najeriya

2. Gaza samun 25% na kuri'u a jiha ko daya a zaben shugaban kasa da ya gabata, sannan gaza samun 25% na kuri'u a karamar hukuma ko daya a zaben gwamnonin jihohi 36

3. Gaza cin zabe a yanki daya a zaben shugaban karamar hukuma a kananan hukumomi 774, gaza cin kujerar dan majalisa daya a jihohin Najeriya da gaza cin kujeran kansila ko daya a fadin tarayya

Jam'iyyun da suka rage sune:

Jam'iyyar Accord

Jam'iyyar Action Alliance AA

Jam'iyyar African Action Congress AAC

Jam'iyyar ADC

Jam'iyyar APC

Jam'iyyar ADP

Jam'iyyar APGA

Jam'iyyar APM

Jam'iyyar LP

Jam'iyyar NNPP

Jam'iyyar NRM

Jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PRP

Jam'iyyar SDP

Jam'iyyar YPP

Jam'iyyar ZLP

Jam'iyyar BP

Jam'iyyar APP

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng