EFCC Ta Kama 'Shugaban' Masu Safaran Sassan Jikin Bil Adama

EFCC Ta Kama 'Shugaban' Masu Safaran Sassan Jikin Bil Adama

- Hukumar Yaki da Rashawa ta EFFC ta kama wani mai shugaban masu safarar mutane

- Wanda ake zargin yana sojan gona a matsayin likita tare da siyan sassan mutane musamman koda

- Hukumar ta sha alwashin kama ragowar yan damfarar da suke aikata wannan mummunan aikin tare

Hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anati, EFCC ta kama wani da ake zargi da safarar sassan mutane, rahoton The Cable.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce wanda ake zargin shine shugaban wata kungiya da ke siyarwa da mutane masu bukatar sassan su ke kuma siya a wajen wanda ke son siyarwa.

EFCC Ta Cafke Shugaban Masu Safaran Sassan Jikin Mutane
EFCC Ta Cafke Shugaban Masu Safaran Sassan Jikin Mutane. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Ukaeje John Emeka, wanda ake zargin shine shugaban wanda kuma aka sani da Dr Phil, an kama shi a watan Afrilu bisa zargin yin karyar shi likita ne don siyan sassan mutane kamar koda.

DUBA WANNAN: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

"A binciken da hukumar ta gudanar ta gano cewa wanda ake zargin shi ne ke jagorantar wata tawagar yan damfara masu ikirarin su likitoci ne, wanda suke da inda suke ajiye sassan mutane musammnan koda don saye ko sayarwa," kamar yadda rahoton yake.

"Wanda abun yafi shafa sune masu matsalar koda da kuma wanda ke son siyar da kodar su a Najeriya, Indiya, Pakistan, Indonesia da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

"Daga cikin abubuwan da aka samu a wajen wanda ake zargin akwai: Passport din tafiye tafiye na Najeriya da na Cote D'ivore, katin cirar kudi guda tara, bakar Laptop kirar HP, waya kira Tecno L9 plus, waya kirar Samsung Galaxy J8, da kuma mota ruwan toka kirar Lexus ES 330."

Hukumar tayi alwashin kama ragowar yan damfarar da yake aiki tare da su.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel