Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

- Adamu Garba, ya ce bukaci Sheikh Gumi ya yi wa ƴan Nigeria bayanin matsayinsa kan ƴan bindiga da ƴan ta'adda

- Tsohon mai neman takarar shugabancin kasar ya yi wannan tambayar ne yayin martani kan kalaman Gumi ne cewa CBN ta bada N500m a bawa yan bindiga

- A baya-bayan dai mutane a dandalin sada zumunta suna damuwarsu kan yadda Sheikh Gumi ke cigaba da neman a yi wa ƴan bindiga afuwa da biyansu kudi

Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba ya ce malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya fito fili ya fayyace wa ƴan ƙasa idan yana tare da Nigeria ne ko ƴan ta'adda da ƴan bindiga.

Hakan ya biyo bayan shawarar da Gumi ya baiwa gwamnatin tarayya na cewa ta karbo Naira miliyan 100 domin ayi amfani da shi don ceto ɗaliban da ƴan bindiga suka sace a Jami'ar Greenfield a Kaduna.

Gumi ya fito fili ya faɗa mana idan ƴan bindiga ya ke yi wa aiki, Adamu Garba
Gumi ya fito fili ya faɗa mana idan ƴan bindiga ya ke yi wa aiki, Adamu Garba. @adamugarba
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

Bayan hakan ya kuma yi kira ga gwamnati ta yi wa ƴan bindigan afuwa yana mai cewa hakan zai saka su ajiye makamansu.

Wani a Twitter mai suna @Yemi_News247 ya janyo hankalin Garba kan abin da Gumi ke aikatawa a baya-bayan nan inda ya ke mamakin ganin DSS ba ta kama shi ba.

Ya rubuta, "@adamugarba mene za ka iya cewa kan abin da Gumi ke yi a baya-bayan nan? A hankali yana zama sakataren kuɗi na ƴan bindiga /ministan na ƴan bindiga da biyan kuɗin fansa. Abin kunya ne ganin miyagu sunyi kutse a DSS. Kaicon ƙasa ta."

KU KARANTA: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

A martaninsa, Garba ya ce, "Ina tunanin ya kamata Gumi ya yi bayani ƙarara shin yana tare da ƴan bindiga/ƴan ta'adda ne ko mutanen Nigeria."

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164