Da Ɗumi-Ɗumi: Allah Ya Yi Wa Ɗan Fasto Enoch Adeboye Rasuwa

Da Ɗumi-Ɗumi: Allah Ya Yi Wa Ɗan Fasto Enoch Adeboye Rasuwa

- Dan gidan Fasto Enoch Adeboye, Fasto Dare Adeboye ya rasu a ranar Laraba a garin Eket a jihar Akwa Ibom

- Marigayi Dare Adeboye mai shekaru 42 ya kwanta barci ne amma da safiya ta yi sai bai farka ba a cewar majiyoyi

- Shugaban sashin watsa labarai na cocin RCCG, Fasto Olaitan Olubiyi, a safiyar ranar Alhamis ya tabbatar da rasuwar Dareboye Rasuwa

Pastor Dare Adeboye, ɗan shugaban cocin Redeemed Christian Church of God worldwide, RCCG, Enoch Adeboye ya riga mu gidan gaskiya.

The Punch ta ruwaito cewa Dare mai shekaru 42 ya mutu cikin barcinsa a ranar Laraba a Eket, jihar Akwa Ibom inda ya ke zaune da iyalinsa.

Da Ɗumi-Ɗumi: Allah Ya Yi Wa Ɗan Fasto Enoch Adeboye Rasuwa
Da Ɗumi-Ɗumi: Allah Ya Yi Wa Ɗan Fasto Enoch Adeboye Rasuwa. Hoto: @TheHGService
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

Majiya ƙwaƙwara daga cocin ta ce faston ya yi wa'azi a ranar Talata kafin ya rasu ranar Laraba.

An ce ya kwanta a gadonsa da dare amma kuma bai farka ba.

"Bai yi rashin lafiya ba kuma bai koka cewa wani abu na damunsa ba. An gayyaci fastoci su yi masa addu'a amma hakan bai sauya komai ba," in ji majiyar.

Shugabannin cocin da dama sun tabbatar da rasuwar amma sun ce ba a basu izinin yin magana a kai ba.

Shugaban sashin watsa labarai na cocin, Fasto Olaitan Olubiyi, a safiyar ranar Alhamis ya tabbatar da rasuwar Dare.

KU KARANTA: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

Ya ce, "Da gaske ne. Lamarin ya faru a garin da Eket ke zaune. Bani da cikakken bayani a yanzu. Watakila kafin yamma za mu fitar da sanarwa."

Idan da yana da rai, zai cika shekaru 42 a watan Yuni.

Dare ya rasu ya bar matar aure da yara.

A bara yayi bikin cikarsa shekaru 42, mahafinsa Adeboye a dandalin sada zumunta na Facebook ya kira shi dan baiwarsa na farko.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel