Magoya bayan Tinubu sun zargi Gwamnan APC da yi wa Jam’iyya da Tinubu makarkashiya

Magoya bayan Tinubu sun zargi Gwamnan APC da yi wa Jam’iyya da Tinubu makarkashiya

- Sanata Adedayo Adeyeye ya ragargaji Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi

- Shugaban kungiyar SWAGA ya maida martani kan dakatar da Clement Afolabi

- SWAGA ta na zargin Gwamnan da kokarin kassara Jagoran APC, Bola Tinubu

Tsohon mai magana da yawun bakin sanatocin Najeriya, Adedayo Adeyeye, ya zargi gwamna Kayode Fayemi da neman karya jam’iyyar APC.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Sanata Adedayo Adeyeye ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC su yi wa gwamnan Ekiti magana ya shiga taitayinsa.

Adedayo Adeyeye wanda shi ne shugaban kungiyar SWAGA masu goyon-bayan Bola Tinubu ya yi takara ya fitar da jawabi ne ta bakin wani hadiminsa.

KU KARANTA: Rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Da yake magana a madadin shugaban wannan tafiya, Gboyega Adeoye, ya soki kalaman da gwamna Kayode Fayemi ya yi a kan jam’iyyar APC.

Gboyega Adeoye ya fitar da wannan jawabi ne ranar Laraba, a garin Ado Ekiti, jihar Ekiti.

Sanata Adeyeye ya maida raddi ne kan tunbuke shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ado Ekiti, Clement Afolabi, da aka yi saboda huldarsa da SWAGA.

Tsohon ‘dan majalisar ya ke cewa: “Muna tir da layin da Fayemi ya dauka wanda ya sauka daga kan turbar damukaradiyya, muna kiran a ja-kunnensa.”

KU KARANTA: Ana kutun-kutun za a dakatar da Shugaban APC saboda hada-kai da Tinubu

Magoya bayan Tinubu sun zargi Gwamnan APC da yi wa Jam’iyya da Tinubu makarkashiya
Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi Hoto: @KFayemi
Asali: Twitter

“Muna kira ga maza da matan jam’iyyarmu a fadin kasar nan, su yi alaka da SWAGA hankali kwance.”

“SWAGA ita ce jam’iyyar APC, kuma jam’iyyar APC ita ce SWAGA. Babu yadda mutum zai yi zagon-kasa don ya na goyon bayan ‘dan takarar jam’iyya.”

Adeyeye wanda ya rike Ministan ayyuka a Najeriya ya zargi Fayemi da kitsa sharri, ya zargi Gwamnan da neman kassara jigon APC, Bola Tinubu.

Tsohon ‘Dan Majalisar Zamfara, Aminu Sani Jaji ya fadi hanyar da Jam’iyya za ta bi ta rike mulki bayan 2023. Sani Jaji ya ce ba ya goyon-bayan kama-kama.

‘Dan siyasar na jihar Zamfara ya ce a 2023, duk wanda ya iya allonsa ya wanke kurum, a maimakona a ware wani yanki a ce an basu damar takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng