Boko Haram: 'Yan majalisar dattawa sun gigice bayan sanarwar za a kai farmaki

Boko Haram: 'Yan majalisar dattawa sun gigice bayan sanarwar za a kai farmaki

- Hankulan 'yan majalisar tarayya Najeriya ya tashi sakamakon sanarwar da aka bada na yuwuwar kai farmakin Boko Haram Abuja

- An gano cewa akwai shirin da 'yan ta'addan suke yi na kai farmaki majalisar dattawa, hukumomin gwamnati da sauran wurare masu muhimmanci

- Tuni dai jami'an tsaro suka fara bincike tare da bankado lamarin kuma an shawarci 'yan majalisar da su sauya hanyar shiga

Sanar da 'yan majalisa da aka yi cewa akwai yuwuwar mayakan Boko Haram su kai farmaki majalisar dattawa da sauran wurare masu muhimmanci a Abuja ya firgita su.

Kamar yadda The Punch ta wallafa,'yan majalisar wakilai masu yawa a ranar Laraba sun tabbatar da cewa an sanar da su batun kai harin.

Daya daga cikinsu wanda ya fito daga jihar Kudu maso yamma, yace zai takaita zuwa majalisar.

"Akwai maganar tsaro da aka yi mana yau. Na shirya barin nan. Zan dinga zuwa ne idan manyan abubuwa sun taso kuma an bukaci zuwa na. Babu inda mutum zai tsira a kasar nan," yace.

Tuni dai aka raba sanarwar yuwuwar harin ga 'yan majalisar gaba daya.

Sanarwan an tura ta ne ga kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila, sauran jiga-jigan majalisar da sauran mambobi.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13

Boko Haram: 'Yan majalisar dattawa sun gigice bayan jin rade-radin za a kai farmaki
Boko Haram: 'Yan majalisar dattawa sun gigice bayan jin rade-radin za a kai farmaki. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna

Sanarwan mai kwanan wata 4 ga Mayun 2021 wanda shugaban kwamitin tsaro na majalisar ya fitar, Usman Shiddi, yace an gano cewa akwai shirin kai hari da ake yi ga manyan wurare, cibiyoyin gwamnati da kadarorinta a Abuja.

"A sakamakon wannan bayanin sirrin, ina shawartar dukkan 'yan majalisa da su dinga amfani da kofar shugaban kasa domin shige da fice.

“An yi hakan ne domin gujewa cunkoson da ake samu wasu lokuta a hanyar shiga tunda ana iya amfani da wannan cunkoson wurin kai farmaki.

“Hukumomin tsaro a halin yanzu suna kan lamarin domin bankadowa tare da shawo kan matsalar," yace.

A wani labari na daban, Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne 'yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng